COVID-19: Almajirai 30 sun tsere daga cibiyar killacewa ta Jigawa

COVID-19: Almajirai 30 sun tsere daga cibiyar killacewa ta Jigawa

Almajirai har 30 wadanda aka killace a sansanin 'yan bautar kasa na karamar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa sun tsere a daren Litinin.

Wata majiya wacce take daga cikin kwamitin yaki da cutar coronavirus ta jihar ce ta sanar da gidan na Channels.

Ya kara da cewa an cafko dukkansu kuma an mayar da su cibiyar killacewar.

Kamar yadda yace, iyayen yaran sun taka rawar gani wajen damko yaran bayan tserewarsu.

A ranar 22 ga watan Afirilu, gwamnatin jihar Kano ta kwashe a kalla almajirai 500 ta mayar dasu jihar Jigawa don tabbatar da kiyaye dokar nisantar juna don gujewa yaduwar muguwar cutar coronavirus.

A ranar Litinin, gwamnatin jihar Gombe ta bi sahun jihar Kano inda ta mayar da almajirai sama da 50 jihar.

Gwamnatin jihar Jigawa ta yanke hukuncin killacesu na kwanaki 14 kafin tabbatar da lafiyarsu don mika su ga iyayensu.

COVID-19: Almajirai 30 sun tsere daga cibiyar killacewa ta Jigawa

COVID-19: Almajirai 30 sun tsere daga cibiyar killacewa ta Jigawa
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari

A wani labari na daban, wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar rufe jihar saboda annobar Coronavirus.

Shugaban ya ce: "A dangane da jihar Kano, na bada umarnin rufe ta gaba daya na makonni biyu tun daga yanzu.

"Gwamnatin tarayya za ta tura duk wani abu da ake bukata don shawo kai da hana yaduwar annobar zuwa jihohin da ke makwabtaka da Kano."

A tattaunawa ta daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya yi da mazauna garin, sun bayyana cewa wannan babban ci gaba ne.

Habibu Umar, mazaunin yankin Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ya ce wannan hukuncin ne mafi cancanta ballantana wajen tsayar da yaduwar cutar.

Umar ya ce sakamakon rashin bin dokar hana zirga-zirga da nisantar juna da aka yi a jihar da farko, hakan ne ya kawo bukatar rufe jihar kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel