Gwamnatin jahar Nassarawa za ta kwashe almajirai 63,000 zuwa jahohinsu na asali

Gwamnatin jahar Nassarawa za ta kwashe almajirai 63,000 zuwa jahohinsu na asali

Gwamnatin jahar Nassarawa ta bayyana shirinta na kwashe almajirai 63,000 yan kasa da shekara 10 daga jahar don mayar dasu zuwa jahohinsu na asali, kamar yadda gwamnatin ta tabbatar.

Daily Nigerian ta ruwaito kwamishiniyar kula da harkokin mata, Halima Jabiru ce ta bayyana haka yayin da take ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwar jahar a garin Lafia.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Sultan ya bukaci Musulmai su fara addu’o’in neman agaji daga Allah Read

Halima ta ce akwai akalla almajirai 63,000 dake gararamba a titunan jahar, don haka gwamnati ta ga dacewar mayar dasu ga iyayensu . idan za’a tuna, Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nassarawa ya samar da dokar daurin shekara 10 a gidan yari ga iyayen da aka kama yaronsu yana bara a jahar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake rattafa hannu kan dokar haramta garkuwa da mutane a jahar da kuma dokar kare kananan yara, haka zalika gwamnan ya haramta barace barace, kuma ya yi alkawarin inganta karatun tsangaya a jahar.

"Wadanda ke bara a yanzu a kan titunanmu za mu daukesu zuwa makaranta domin inganta rayuwarsu. Amma duk wanda ya sake kawo dansa almajiranci jahar Nassarawa daga wata jaha sai mun daure shi a kurkuku.” Inji shi.

Gwamna Sule ya kara da cewa ba zasu hukunta yaran da suka kama yana bara ba, amma iyayensu zasu fuskanci fushin hukuma, saboda wannan ya nuna rashin dacewar su haifi yaran tun farko sakamakon ba za su iya kulawa da su ba.

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Jama’atil Nasril Islam, JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Maris a garin Kaduna.

Sultan ya yi kira ga Musulmai su dage da tsafta tare da bin duk wasu hanyoyin tsaftace kawunansu don kauce ma yada cutar Coronavirus, sa’annan ya yi kira ga Malamai da limamai su cigaba da wayar da kawunan jama’a akan cutar a dukkanin salloli biyar na kowanne rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel