Rana Dubu ta Barawo: 'Yan Sanda a jihar Niger sun yi Ram da Barayin ATM
- Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kwarewa wajen musanyawa bayin Allah katin ATM
- An kama Philip Adefemi da Joseph Michael bayan sun yiwa wani bawan Allah sane tare da cirar ₦400,000 jim kadan bayan sace masa katin
- Kakakin rundunar, SP Wasi'u Abiodun ya bayyana cewa yanzu haka daya daga wadanda ake zargi ya arce, amma ana ci gaba da binciken sauran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Niger- Rundunar 'yan sanda a jihar Niger ta yi nasara kama bata garin da ke musanyawa mutanen katin cirar kudi na ATM.
An kama wasu mutum biyu dauke da katinan ATM guda 42 da su ka sace daga hannun bayin Allah a jihar.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa kakakin rundunar SP Wasiu Abiodun ya ayyana wadanda aka kama da Philip Adefemi mai shekaru 46 da Joseph Michael mai shekaru 42.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama barayin katin ATM
Kakakin rundunar 'yan sandan Niger, SP Wasiu Abiodun ya ce jami'ansu da ke caji ofis din Bida ne su ka samu nasarar damke bata-garin biyu.
The Nation ya wallafa cewa kamen ya biyo bayan koken wani bawan Allah da ya ce ya sanya katin ATM dinsa, amma kudin bai fito ba, daga nan ne wani a bayansa ya yi kokarin taimakonsa, ashe ya musanya katin.
"Bayan wani lokaci ne aka aikowa da mai katin sakon cirar kudi N400,000, inda nan take ya kai kokensa ofishin 'yan sanda,"
- SP Abiodun.
Zuwa yanzu dai mazan biyu na hannun jami'an tsaro ana zurfafa bincike, yayin da wani da ake zargi suna satar tare, Bala ya cika wandonsa da iska.
Mata ta karar da kudin asusun mijinta
A baya mun ba ku labarin wata mata da ta yi amfani da katin ATM da mai gidanta ya bata wajen sayen kayan abincin da gida ke bukata.
Israel Obinna Ugwu ya wallafa a shafinsa na facebook cewa dukkanin albashinsa matar ta kwashe tas wajen cefanen kayan abinci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng