Mafi Karancin Albashi: 'Ka da Gwamnati ta Kuskura ta Mana Tayin N100,000,' TUC

Mafi Karancin Albashi: 'Ka da Gwamnati ta Kuskura ta Mana Tayin N100,000,' TUC

  • Kungiyoyin kwadagon kasar nan sun bayyana cewa sun shirya halartar taron ci gaba da duba kan batun mafi karancin albashi a kasar nan
  • A gobe Talata ne kwamitin da gwamnatin tarayya ya kafa kan mafi karancin albashi zai sake zama da NLC da TUC bayan sun yi fatali da tayin farko
  • Kwamitin dai ya yi tayin N48,000 lamarin da kungiyar ta yi fatali da shi, tare da bayyana cewa ba za ta amince da ko da tayin N100,000 ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Kungiyoyin kwadago sun ce gobe Talata zasu halarci taron ci gaba da tattauna batun sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya za ta sake zama da NLC kan mafi karancin albashi

Mataimakin shugaban kungiyar TUC ta manyan ma’aikatan kamfanoni da masana’antu, Mista Etim Okon, ya tabbatar da haka yau a Abuja.

Kungiyar kwadago
Kungiyoyin kwadago sun gargadi gwamnati kan N100,00 a matsayin mafi karancin albashi Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

NLC, TUC za su koma teburin albashi

Kungiyoyin NLC da TUC sun fice daga taron karshen makon jiya, bayan da abokan tattaunawa na bangaren gwamnati suka yi musu tayin N48, 0000 a matsayin sabon mafi karancin albashi a kasar nan, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin kwadagon sun yi fatali da tayin, inda suka ce abin ya nuna tamkar wasa ake yi da al’amarin ma’aikata a Nijeriya.

‘Ba za mu karbi N100,000 ba,’ NLC

Kungiyar kwadago ta NLC ta gargadi gwamnati da ka da ta kuskura ta yi musu tayin N100,000 a matsayin mafi karancin albashi.

Shugaban bangaren yada labaran NLC, Benson Upah ne ya bayyana hakan kamar yadda Vanguard News ta wallafa labarin yau.

Kara karanta wannan

"N48,000 Tayin almajirai ne": Shehu Sani ya caccaki gwamnati kan mafi karancin albashi

A kalamansa:

“Muna fatan gwamnati za ta dauki batun nan da gaske na biyan mafi karancin albashi.”

Ya ce a N615,000 da su ka nema ba su tsawwala ba, domin kudin ba zai kai ko ina ba.

N48,000: TUC ta ga rashin lissafin gwamnati

Mun ba ku labarin cewa kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC ta ga bayyana tayin mafi karanacin albashin da gwamnatin tarayya ta yi da rashin lissafi.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya ce tayin N48,000 da gwamnatin ta yi ya nuna karara cewa ba a shirya tattaunawa da kungiyoyin kwadago ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.