'Yan Bindiga Sun Sauya Salon Kai Hare Hare a Garuruwan Katsina, Dikko Radda Ya Magantu
- Gwamna Dikko Radda ya ce 'yan bindiga sun sauya salon da suke amfani da shi wajen kai hare-hare a garuruwan jihar Katsina
- Gwamnan ya bayyana hakan ne duk da yana cewa gwamnatinsa ta rage yawan ayyukan ‘yan bindiga a jihar da kashi 70
- Mai girma Dikko ya yi kira da a samar da 'yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa, Yola - Gwamnan Katsina, Dikko Radda, ya ce 'yan bindiga a yanzu sun sauya salon da suke amfani da shi wajen kai hare-hare a garuruwan jihar.
Mai girma Dikko ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Asabar yayin wata ziyara da ya kai Yola, babban birnin Adamawa.
Radda ya nemi a kafa 'yan sandan jihohi
Gwamnan jihar na Katsina ya ce an samu raguwar ‘yan fashin ne saboda “karfin hadin gwiwa” tsakanin jami’an tsaro, jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sa:
"Gwamnatina ta rage yawan ayyukan ‘yan bindiga a jihar Katsina da kashi 70 cikin 100 a cikin shekara daya."
Mai girma gwamnan ya ce jihar ta aiwatar da matakan magance hare-hare a garuruwan da ke da nisa da birane, inda ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai magance lamarin.
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samar da 'yan sandan jihohi domin kara karfafa yaki da rashin tsaro a kasar.
"Yan bindiga sun sauya salo" - Dikko Radda
Gwamnan ya ce duk da raguwar ayyukan ta'addancin, ‘yan bindigar sun bullo da wata sabuwar dabara ta kai hare-hare a yankunan da ke da wahalar shiga jihar.
NAN ta ruwaito Radda yana cewa:
“Yan bindigar sun sauya salon da suke bi na zuwa kauyukan da ke da wuyar isa, suna kona gidaje da kashe mutane."
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su baiwa fannin ilimi fifiko domin samun ci gaba a kasar nan, in ji rahoton jaridar Tribune.
'Yan sandan jihohi: 'Yan majalisu sun goyi baya
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar shugabannin majalisun jihohi 36 sun yi wata ganawa a Abuja a makon jiya, in da suka amince da kudurin samar da 'yan sandan jihohi.
Kakakin majalisar jihar Oyo kuma shugaban taron, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin ya sanya hannu kan sanarwar da kungiyar ta fitar yana mai cewa hakan zai magance matsalolin tsaro a kasar.
Asali: Legit.ng