"Mun Ci Karfinsu": Gwamna Ya Bugi Kirji Kan Markaɗe Ƴan Ta'adda a Katsina

"Mun Ci Karfinsu": Gwamna Ya Bugi Kirji Kan Markaɗe Ƴan Ta'adda a Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bugi kirji kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu kan ta'addanci a jihar
  • Radda ya ce gwamnatinsa ta rage ta'addanci da 70% wurin amfani da dabarun yaki da kuma hadin guiwar jami'an tsaro daban-daban
  • Gwamnan ya bukaci kirkirar ƴan sandan jihohi inda ya ce hakan zai taimaka wurin yaki da ta'addanci da ake fama da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya ce sun ci galaba kan ta'addanci a jihar.

Gwamnan ya ce akalla ya dakile matsalar tsaron jihar da 70% a cikin shekara daya da ya yi a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

Gwamna ya bayyana nasarorin da ya samu kan ta'addanci a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina ya ce sun rage ta'addanci da 70% a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda.
Asali: Facebook

Katsina: Yadda aka murƙushe ƴan ta'addanci

Radda ya bayyana haka ne a yau Asabar 18 ga watan Mayu yayin hira da ƴan jaridu a birnin Yola na jihar Adamawa, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dikko ya ce nasarar bata rasa nasaba da hadin kan jami'an tsaron gwamnati da kuma yan banga wurin tabbatar da dakile matsalar tsaro a jihar, cewar The Guardian.

Dabarun yaki da ake bi a Katsina

"Lokaci ya yi da ya kamata a kirkiri yan sandan jihohi domin ci gaba da yakar ta'addanci a Arewacin Najeriya."
"Mun yi nasarar dakile ta'addanci da 60% zuwa 70% saboda irin matakan da muke ɗauka ganin yadda suka sauya taku."
"Maharan yanzu sun fusata inda suke zuwa ƙauyuka suna hallaka mutane da kuma kona su, mun samo dabarun yakarsu."

- Dikko Umaru Radda

Wannan martani na gwamnan na zuwa ne yayin da ƴan bindiga suka addabi jihar musamman a yankunan karkara.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamna ya kuma ɗaga yatsa ga Wike, ya bugi kirji kan jikkata abokan gaba

Ƴan bindiga sun hallaka sojoji a Katsina

A wani labarin, wasu yan bindiga sun kai farmaki kan sansanin sojoji a jihar Katsina inda suka hallaka akalla dakaru guda biyar.

Lamarin ya faru ne a kauyen Yar Malamai da ke karamar hukumar Faskari a jihar a makon da ya gabata kamar yadda rundunar sojoji ta tabbatar.

Yayin harin, sojoji da dama sun jikkata inda suka tsere daga sansanin bayan farmakin bazata da aka kawo musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.