Gwamnati Ta Aika Muhimmin Sako Ga Dalibai, Za a Fara Ba da Rancen Kudin Karatu
- Hukumar kula da asusun ba da lamunin karatu (NELFund) ta sanar da ranar bude shafin yanar gizo na neman rancen kudin karatu
- Hukumar NELFund ta ba da tabbacin cewa daliban Nigeria za su iya fara neman rancen kudin karatu a ranar 24 ga watan Mayu, 2024
- Babban daraktan NELFUND, Mista Sawyerr, ya ce daga yanzu dalibai za su cika burinsu na yin karatu ba tare da matsaloli na kuɗi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ya sanar da ranar bude shafin yanar gizo domin ba daliban Nigeria damar fara neman rancen kudin karatu.
Hukumar kula da asusun ba da lamunin karatu na Najeriya (NELFund) wadda ta bayyana hakan ta ce za a bude shafin ne a ranar 24 ga watan Mayu, 2024.
Matsalar kudin karatun dalibai ta kare
Babban daraktan NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Sawyerr ya ce ba da damar neman rancen kudin ya nuna an samu nasara a yunkurin Shugaba Bola Tinubu na ganin daukacin daliban Najeriya sun samu ilimi cikin sauki.
A cewar Mista Sawyerr:
"Ta cikin shafin, ɗalibai za su iya samun lamuni domin cika burinsu na yin ilimi ba tare da matsalolin kuɗi ba."
Yadda dalibai za su nemi lamunin
Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun mai kula da harkokin yada labarai na asusun, Nasir Ayitogo, ta ce shafin zai samar da hanya mai sauki ga dalibai yayin cike bukatun neman lamunin.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dalibai za su iya shiga shafin hukumar na yanar gizo ta www.nelf.gov.ng domin cike fom din lamunin.
Haka zalika dalibai na iya tuntuɓar sashen taimako na hukumar ta imel a kan info@nelf.gov.ng ko kuma shafukansu na soshiyal midiya.
Tinubu ya nada shugaban NELFund
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Jim Ovia, a matsayin shugaban hukumar kula da asusun lamunin karatu ta Najeriya (NELFund).
Mista Ovia shi ne wanda ya kafa bankin Zenith kuma hamshakin dan kasuwa mai daraja, wanda ake fatan zai karfafi guiwar dalibai domin su samu ilimi mai zurfi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng