Filin Jirgin Sama: Shugaba Bola Tinubu Zai Ba Wasu Jihohin Arewa N24.6bn

Filin Jirgin Sama: Shugaba Bola Tinubu Zai Ba Wasu Jihohin Arewa N24.6bn

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya rubuta wasika ga majalisar dattawa domin neman izinin biyan jihohin Nasarawa da Kebbi N24.6bn
  • Mai girma Shugaban kasar ya bayyana cewa za a biya jihohin kudaden ne bayan gwamnatin tarayya ta karbi filayen jiragen saman su
  • Ya kuma bayyana adadin da ko wace jiha za ta samu da yadda doka ta ba gwamnatin tarayya izinin karbar filayen jirage

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin majalisar tarayya domin biyan jihohin Nasarawa da Kebbi N24.6bn.

Shugaban kasar zai biya jihohin zunzurutun kudin ne domin karbar filayen jiragen samansu da gwamnatin tarayya ta yi.

Kara karanta wannan

Atiku ya nemi takawa Bola Tinubu burki kan taba kudin ’yan fansho ayi ayyuka

Tinubu
Gwamnatin tarayya za ta biya Nasarawa da Kebbi N24.6b kan karbar filayen jiragen sama. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kasar ya umurci majalisar ta yi gaggawar amincewa da kudirin nasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Kudin da kowace jiha za ta samu

A cikin N24.6b din gwamnatin jihar Kebbi za ta samu sama da N15bn domin karbar filin jirgin saman Ahmadu Bello da ke birnin Kebbi.

Ita kuma jihar Nasarawa za ta samu N9bn domin domin karbar filin jirgin saman ta da ke Lafiya.

Meyasa gwamnatin tarayya za ta biya kudin?

A cikin wasikar da shugaban kasar ya aikawa majalisar, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta riga ta karbi mallakar filayen jiragen saman jihohin.

Saboda haka a bisa doka dole ne a biyasu kudin da suka kashe wurin gina su, cewar rahoton jaridar Premium Times.

Kuma ya kara da cewa dokar kasa ta ba gwamnatin tarayya izinin mallakar filayen jiragen sama a Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ganduje zai sarara bayan kotu ta dakatar da bincikensa

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa majalisar zartarwa ta tarayya ma ta amince da mayarwa jihohin kudin da suka batar.

Saboda haka ne shugaban kasar ya rubuta wa majalisar neman amicewa da biyan kudin tun da filin ya bar hannun jihohin.

Tinubu zai fara biyan harajin jirgin sama

A wani rahoton kuma, kun ji cewa yayin da ake korafe-korafen kan ƙaƙaba haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke yi, shugaban bai ware kansa ba a kan lamarin.

Tinubu ya soke dokar da ta hana shi da mataimakinsa, Kashim Shettima biyan harajin a filayen jiragen saman kasar yayin amfani da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel