An Yi Zanga-Zanga a Filin Jirgin Sama Na Kano Saboda Dalili 1

An Yi Zanga-Zanga a Filin Jirgin Sama Na Kano Saboda Dalili 1

  • Fusatattun fasinjoji sun yi zanga-zanga a filin jirgin sama na Kano saboda jinkirta tashin jirgin karfe 1:00 na rana zuwa Legas da kamfanin jirgin Max Air ya yi
  • An rahoto cewa kamfanin jirgin bai sanar da fasinjoji wannan sabon tsari ba lamarin da yasa suka yi cirko-cirko a filin jirgi kusan awanni biyar
  • Wasu daga cikin fasinjojin sun koka akan yadda aka rusa musu shirin su domin harda wani mai zuwa ganin likita wanda har sai da zafin ciwo ya dungi cinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kano - Fusatattun fasinjoji a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, sun gudanar da 'yar zanga-zanga kan jirgin Max Air sakamakon jinkiri da aka samu wajen tashinsu zuwa Legas.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Matasa a Borno sun yi barazanar shiga Boko Haram, bayanai sun fito

An shirya jirgin mai lamba VM1645 zai tashi da misalin karfe 1:00 na rana, amma sai aka dage ba tare da an sanar da fasinjoji kafin lokaci ba, lamarin da ya jefa su cikin takura na kusan awanni biyar.

Fasinjoji sun yi zanga-zanga a filin jirgin sama na Kano
An Yi Zanga-Zanga a Filin Jirgin Sama Na Kano Saboda Dalili 1 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rashin samun bayani daga bangaren kamfanin jirgin ya kara tabarbarar da kamarin, wanda hakan ya haifar da hatsaniya a bangaren tashin jiragen cikin gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me fasinjojin suka ce?

Mista Abubakar Muhammad wanda yana daya daga cikin fasinjojin da abin ya shafa, ya ce ya kamata ya kasance a Legas domin duba lafiyarsa.

"Jingirin ya haifar mani da radadi mai yawan gaske," cewarsa yayin da yake nuna muhimmancin tafiyarsa.

Haka kuma, wani fasinja mai suna Mista Yusuf Sani ya nuna rashin jin dadinsa kan yawan jinkiri da ake ci gaba da samu wajen tashin jirgin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Jirgi maƙare da mutane ya gamu da mummunan hatsari a jihar APC, rai ya salwanta

Ya ce:

"Haka suka kawo mana jinkiri a baya, me zai sa a jinkirta tashin jirgi ko a sauya lokaci ba tare da an sanar da mutane ta yadda ya dace ba?"

Ku tuna cewa, a watan Yulin 2023 Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) yi jawabi kan kamfanoni.

NCAA ta bayyana cewa kamfanin Air Peace ya jinkirta yawan tashin jiragen cikin gida a cikin kwata na farko na 2023, inda ya yi jigila sau 6521 tare da jinkirta 3,754 (kashi 51 cikin dari).

Max Air ne ke bin sa inda ya yi jigila sau 1,565 tare da jinkirin sau 1,013 (kashi 60 cikin dari), rahoton Leadership.

Fasinjoji sun afka ofishin Azman a Kano

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa fusatattun fasinjojin jirgin sama na Azman sun tayar da kura a ofishin kamfanin jirgin a ranar Litinin bisa fasa tashin jirgin karfe 7 na safe zuwa Legas.

An samu bayanai akan yadda kamfanin jirgin ya sanar da fasinjojin batun fasa tafiyar ta sakon yanar gizo ana saura mintuna kadan da lokacin tashin jirgin ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel