Kisan sojoji: Rundunar Sojoji Ta Saki Sunaye da Hotunan Mutum 7 da Ake Nema Ido Rufe

Kisan sojoji: Rundunar Sojoji Ta Saki Sunaye da Hotunan Mutum 7 da Ake Nema Ido Rufe

  • Dakarun sojoji a Najeriya sun sanar da mutane takwas da suke nema ruwa a jallo kan kisan sojoji a jihar Delta
  • Rundunar ta fitar da sunayen mutanen ne da suka hada da wani Farfesa da wata mata da sauran mutane shida
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sa daraktan yada labarai na rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta fitar sunayen mutane takwas da ta ke nema ruwa a jallo.

Rundunar ta fitar da sunayen ne kan zarginsu da kisan sojoji 17 a kauyen Okuama da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 17: Tinubu ya fusata, ya ba da sabon umarni ga dattawa da sarakunan Okuama

Sojoji sun fitar da sunayen mutane 8 da suke name ruwa a jallo kan kisan jami'ansu
Rundunar sojoji ta na neman wani Farfesa da mutum 7 kan kisan sojoji a Delta. Hoto: @HQNigerianArmy.
Asali: Twitter

Sunayen wadanda sojojin ke nema

Daga cikin wadanda ake neman akwai Farfesa Ekpekpo Arthur da wata mata, Igoli Ebi da Reuben Baru da Akata Malawa David.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Sinclear Oliki da Clement Ikolo da Dennis Bakriri da kuma Daniel Omotegbono.

Daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba shi ya tabbatar da haka a shafin Facebook a yau Alhamis 28 ga watan Maris.

Sai dai Buba ya ce babu wani kudi da aka saka a matsayin tukuici ga wadanda suka kawo su ko kuma ba da bayanai da za su taimaka a cafke su.

Yadda aka hallaka sojoji 17 a Delta

Wannan sanarwa daga rundunar na zuwa ne bayan kisan wasu sojoji 17 a jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka je kwantar da tarzoma a kauyen Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar.

Kara karanta wannan

Bassirou Faye: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban Senegal mai jiran gado

Kisan sojojin ya ta da ƙura inda wasu ke kiran a dauki mummunan mataki kan haka saboda dakile faruwar hakan a nan gaba.

Tinubu ya ba dattawa Okuama umarni

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci dattawa da sarakunan kauyen Okuama a jihar Delta sa su zakulo wadanda ake zargi da kisan sojoji 17.

Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Laraba 27 ga watan Maris a Abuja yayin jana'izar sojojin da suka mutu.

Shugaban ya ce ba zai taba bari rayukansu ya tafi a banza ba inda ya ce dole a bi musu hakkinsu wurin tabbatar da hukunta masu laifin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel