Gwamnonin Arewa Sun Dira Legas, Sun Shiga Ganawa da Shugaba Tinubu

Gwamnonin Arewa Sun Dira Legas, Sun Shiga Ganawa da Shugaba Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Biyo bayan ganawarsu a fadar gwamnatin jihar Legas da ke Marina, mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya sun gana da Shugaba Tinubu a gidan sa da ke Legas.

Babban mai tallafawa gwamna Sanwo-Olu kan kafofin watsa labarai, Jubril Gawat ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Talata, The Nation ta ruwaito.

Ya rubuta cewa:

"Kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin shugabancin @RealAARahman sun taru a Legas, fadar gwamnatin jihar da ke Marina. Daga nan suka zarce gidan shugaban kasa a Legas.
"Zababben gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo na daga cikin tawagar gwamnonin.

Karin bayani kan labarin na zuwa...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel