SSANU da NASU: Gwamnatin Tarayya za ta Biya Rabin Albashin Ma'aikatan da ta Rike

SSANU da NASU: Gwamnatin Tarayya za ta Biya Rabin Albashin Ma'aikatan da ta Rike

  • Gwamnatin Tarayya ta ce akwai yiwuwar ta biya ma'aikatan ilimi na SSANU da NASU rabin albashisu da suke binta tun 2022
  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan, inda ya ce suna kokarin biyan ma'aikatan domin sama musu sauki
  • Amma za a biya kudin ne idan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da bukatar da suka tura masa na biyan albashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce akwai yiwuwar ta biya ma'aikatan jami'o'in gwamnati rabin albashinsu da suke bin gwamnati.

Ministan Ilimi, Tahir Mamman ne ya bayyana hakan ga Channels tv, inda ya ce za a biya ma'aikatan idan shugaba Tinubu ya amince da hakan.

Kara karanta wannan

Dan Majalisa ya shawaraci takwarorinsa da suka koma jam'iyyar APC a Ribas su yi murabus

Bola Tinubu
Za a biya kudin ne idan Shugaba Bola Tinubu ya amince Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministan ya ce suna sane da cewa ma'aikatan ilimin ƙarƙashin kungiyar SSANU da NASU ba su shiga yajin aiki na tsawon lokacin da malaman jami'o'i suka yi ba a shekarar 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na ƙoƙarin warware matsalar albashin

Ministan ilimin, Farfesa Tahir Mamman ya ce duk da dai an samu tsaiko wajen biyan ma'aikatan ilimin albashinsu, suna ta ƙoƙarin warware matsalar, kamar yadda leadership News ta ruwaito.

Ya ce:

"Gwamnati tana duk abinda zai yiwu wajen sama musu sauƙi."

SSANU, NASU na zargin Gwamnatin da rashin adalci

Dukkanin kungiyoyin malamai masu koyarwa kamar ASUU da na ma'aikatan manyan makarantun da basa shiga aji sun shiga yajin aiki a kokarin ganin gwamnati ta biya musu buƙatunsu.

Amma gwamatin Tinubu ta bijiro da tsarin ba aiki ba biya kan wadanda suka gudanar da yajin aikin.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnan Arewa ya faɗi alamun da ke nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in talakawa a Ramadan

Bayan yajin aikin watanni takwas din, gwamnatin ta amince a biya malaman jami'o'in albashinsu na tsawon watannin da suka yi yajin aikin kamar yadda channels ta ambata.

Sai dai su ma'aikatan karkashin SSANU da NASU na zargin da biyu gwamnatin ta ki biyansu.

SSANU, NASU sun shiga yajin aiki

A watan Maris ƙungiyoyin malaman ma'aikatan manyan makarantu ƙarƙashin SSANU da NASU suka yi barazanar tsunduma yajin aiki.

Hakan yana zuwa ne bayan an biya ma'aikatan da ke karkashin ASUU albashin watanni hudu a lokacin da ake yajin-aiki a jami'o'in kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel