Dalilin da Yasa Dalibar da Aka ci Zalinta a Makarantar Abuja ke Neman Diyyar N500m
- Daliba Namitra Bwala ta nemi makarantarta ta Lead British International School ta biya ta diyyar N500m bayan cin zarfinta da 'yan uwanta dalibai su ka yi
- Lauyoyin dalibar sun zargi makarantar da sakaci wajen bayar da ilimi a yanayi mai kyau da tsaro, wanda haka ne ya bayar da cin zarafin Namitra
- A watan Afrilu ne wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna wasu dalibai na kallon yadda wata daliba ta dinga zabgawa Namitra mari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Dalibar nan da bidiyon cin zalinta ya karade shafukan zumunta, Namitra Bwala ta maka makarantarta ta Lead British International School kotu, ta na neman a biya ta diyyar N500m.
Tun da fari an ga wata daliba ta na ta dallawa Namitra Bwala mari, yayin da wasu daliban ke zagaye da ita suna kallo.
A watan Afrilun da ya gabata ne wata mai amfani da shafin X, @mooyeeeeeee, ta wallafa bidiyon marin da ‘yan ajin Namitra su ka yiwa ma ta, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daya daga abun da ya dauki hankali shi ne yadda wasu daga daliban su ka zuba idanu, har da tofa albarkacin bakinsu amma ba su hana marin ba.
Namitra ta nemi diyyar N500m
Bayan bidiyon cin zalin Namitra Bwala ya bayyana a shafukan sada zumunta, a ranar Litinin ne lauyoyin dalibar su ka shigar da kara gaban kotu suna neman a biya diyyar N500,000,000.
Lauyoyin sun nemi makarantar Lead British ta biya kudin ne bisa zargin gaza samar da ingantaccen yanayin karatu mai inganci da tsaro.
Tun bayan fitar bidiyon masu amfani da shafukan sada zumunta ke ganin rashin kyautawar hukumomin makarantar da daliban da su ka zura idanu har ana cin zalin Namitra, kamar yadda Punch News ta wallafa.
Amma hukumomin makarantar sun ce su na ci gaba da binciken lamarin, kuma za su dauki matakin da ya dace, sun kuma bayyana fatan dalibar ta koma karatu bayan an kammala binciken.
An rufe Lead British School
Mun ba ku labarin cewa hukumomin Lead British School sun rufe makarantar bisa zargin cin zarafin wata daliba Namitra Bwala.
Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda yadda wata daliba ta dinga shararawa dalibar mari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng