Hukumar jami'a ta dakatar da malami a kan zargin cin zarafi da dirka wa daliba ciki

Hukumar jami'a ta dakatar da malami a kan zargin cin zarafi da dirka wa daliba ciki

- Hukumar jami'ar ilimi ta IAUE ta dakatar da wani malami sakamakon yiwa wata daliba ciki

- An samu labarin yadda malamin ya ci wa dalibar zarafi kafin yayi mata cikin

- Bayan cikin da yayi mata, dalibar ta fuskanci wasu matsaloli na lafiya masu tarin yawa

Hukumar jami'ar ilimi ta Ignatius Ajuru (IAUE) ta dakatar da wani malami, Dr Rowland Uchechukwu Igwe, sakamakon yi wa wata daliba ciki.

An samu labarin cewa, malamin ya tsoratar da dalibar kafin yayi mata cikin, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Shugaban jami'ar, Farfesa Ozo-Mekuri Ndimele, ya tabbatar da hukuncin a shafinsa na kafar sada zumuntar Facebook a ranar 24 ga watan Satumba, inda ce dalibar ta fuskanci wahalhalu sakamakon cikin.

Wallafar ta kara da cewa, "Hukumar jami'ar ilimi ta Ignatius Ajuru ta dakatar da wani malami, Dr Rowland Uchechukwu, a kan laifin cin zarafi da kuma tozarta wata daliba wadda hakan ya kaiga yi mata ciki da kuma cutar da lafiyarta."

Shugaban jami'ar, ya wallafa a shafin nasa, "An mika al'amarin hannun kwamitin hukunta malaman jami'a domin cigaba da bincike."

KU KARANTA: Jerin kasashe biyar a duniya da suke da saukin samun aiki

Babbar jami'a ta dakatar da malami a kan zargin cin zarafi da dirka wa daliba ciki
Babbar jami'a ta dakatar da malami a kan zargin cin zarafi da dirka wa daliba ciki. Hoto daga Linda Ikeji
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan jerin motocin alfarma 10 masu matukar tsada a duniya

A wani labari na daban, matashi mai shekaru 23 mai suna Olamilekan Ibidokun, ya bada labarin yadda 'yan kungiyar asiri da ke yankin Ketu ta jihar Legas suka mayar da shi makaho bayan ya ki shiga kungiyar.

Kamar yadda yace, lamarin ya faru a watan Disamban 2016 yayin da suka yi wani shagalin biki a yankin Ketu ta jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Ya yi ikirarin cewa, maharan da suka makantar da shi har a halin yanzu suna yawonsu a titi ba tare da an tabbatar da wani lamari adalci a kansu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: