Gwamnatin Tarayya Ta Hada Kai da Enugu Domin Sarrafa Rogo Zuwa Sinadarin Fetur

Gwamnatin Tarayya Ta Hada Kai da Enugu Domin Sarrafa Rogo Zuwa Sinadarin Fetur

  • A wani yunkuri na ganin an bunkasa harkar noma, gwamnatin tarayya da ta jihar Enugu sun kulla yarjejeniyar noman rogo da sarrafa shi
  • Kwamishinan noma na jihar Enugu, Hon. Patrick Ubru ya ce za a sarrafa rogon ne zuwa sinadarin fetur na 'bioethanol' bayan an noma
  • A yayin da aka kaddamar da noman hekta 1,000 a matsayin gwaji, Hon. Ubru ya ce na dauki matakai na tabbatar da nasarar shirin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Enugu - Gwamnatin jihar Enugu ta yaba da hadin gwiwarta da gwamnatin tarayya kan noman rogo da sarrafa shi zuwa sinadarin fetur na 'bioethanol'.

Gwamnati ta ce tana kara habaka noman rogo a jihar domin bunkasa tattalin arziki, tare da taimakawa wajen magance rashin aikin yi da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama yan bindiga da matsafi da gashin mutum

An fara sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur a Enugu
Hadakar gwamnatin tarayya da jihar Enugu kan sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur ta yi nasara. Hoto: Pituk Loonhong
Asali: Getty Images

Kwamishinan noma, Hon. Patrick Ubru ne ya bayyana haka a Okpanku da ke karamar hukumar Aninri, jaridar The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An noma shekta 1,000 na rogo" - Ubru

Hon. Ubru ya zagaya da wata tawagar gwamnatin tarayya zuwa kamfanonin da ke aikin sarrafa rogo zuwa 'bioethanol' a kananan hukumomin Aninri, Isi-Uzo da Udi na jihar.

Ubru ya sanar da tawagar ce an noma sama da shekta 1,000 na rogo a kananan hukumomin uku a shekarar da ta gabata, wanda aka yi amfani da shi matsayin gwaji na shirin sarrafa rogo zuwa sinadrin fetur.

Ya kuma bayyana cewa kafin a gyara gonakin, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun yi sansanoninsu a wajen inda suke farmakar mazauna kananan hukumomin.

"Za a gina tituna a garuruwan Enugu" - Ubru

Kara karanta wannan

Yayin da ake wahalar man fetur, Gwamna zai rufe gidajen mai da ke kara farashi

Ubru ya ce gwamnatin jihar na kokarin hada kai da gwamnatin tarayya domin kafa sansanin soji a Isi Uzo, yayin da kuma za ta kafa rundunar tsaro ta dakarun gona domin ba da tsaro a gonakin.

Jaridar Leadership ta ruwaito kwamishinan ya kuma bayyana cewa jihar za ta fara aikin gina hanyoyin shiga gonaki masu nisan kilomita 20 a Okpanku.

Ya kara da cewa jihar ta biya kashi 50 cikin 100 na aikin gina titi mai tsawon kilomita 22 daga Ikem a yankin karamar hukumar Isi Uzo zuwa kan iyaka da jihar Benue.

"Abinci zai wadata a Najeriya" - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tabbatar ta wadatar da 'yan Najeriya da abinci.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jihar Neja yayin kaddamar da ginin tituna yana mai cewa gwamnati ta dauki matakai na ganin an inganta noma a fadin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.