Noman rogo na iya maye gurbin mai a Najeriya inji manoma

Noman rogo na iya maye gurbin mai a Najeriya inji manoma

Kungiyar manoma rogo a Najeriya ta ce kasar zata iya samun kudaden shiga da yawansu ya kai naira Tiriliyan 20 duk shekara idan har gwamnatin kasar zata bunkasa noman Rogon.

Shugaban manoman rogo a Najeriya Segun Adewumi, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a babban birnin Najeriya Abuja.

Adewumi ya bukaci gwamnatin kasar ta bunkasa noman rogo ganin cewa ana bukatarsa a Duniya, kuma hakan zai taimakawa Najeriyar fita daga halin koma bayan tattalin arziki da kasar ke fuskanta, ta hanyar daina dogaro kan man fetur.

Shugaban manoma rogon ya ce Najeriya tana amfani da naira biliyan 600 duk shekara, don shigo da sinadarin Ethanol da kuma sitati wadanda za’a iya samar da su cikin kasar.

A cewar Adewumi za’a iya samara da abubuwa daban daban har kashi 20 daga jikin rogo wadanda za’a iya saida su ga kasashen duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel