Babban mota ta murkashe wani mai gyara yayin da ya ke fitsari a gefen titi

Babban mota ta murkashe wani mai gyara yayin da ya ke fitsari a gefen titi

Wata tipa ta markade wani mai gyaran taya dan shekaru 29 a unguwar Akinhan da ke garin Awowo na karamar hukumar Ewekoro na jihar Ogun.

The Nation ta ruwaito cewa wata majiya ta bayyana cewa wani mai mota ne ya kira mamacin, Adeyemi Abiodun da ake yiwa lakabi da Olainukan domin ya gyara masa tayar motarsa da tayi paci a ranar Laraba makonni biyu da suka gabata.

An ce har ya tsallaka babban titin Legas zuwa Abeokuta domin ya tarar da mai motar da zai yi wa gyran.

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

Majiyar ta ce daga nan ne kuma ya ce yana bukatar yin fitsari kuma ya koma gefen yana fitsarin sai wata tipa da birkin ta ya lalace ta bi ta kansa ya mutu nan take.

Dreban tipan ya tsere nan take hakan yasa mafusatan matasa suka tare hanyar suka hana sauran masu tipa wucewa ta wannan titin.

Kamar bayan awanni uku an yi sulhu a unguwar kuma matasan sun bude titin.

An kai gawarsa zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibitin Ifo. 'Yan uwa da abokan arziki sun yi jana'izarsa a ranar Alhamis da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel