Ana sauran yan makonni daurin aurenta, babbar mota ta murkushe kyakkyawar budurwa
An tabbatar da mutuwar wata budurwa yar Najeriya mai suna, Immaculate Okuchu, bayan wata babbar mota ta murkushe ta a unguwar Ajah a jihar Legas.
The Nation ta ruwaito cewa budurwar na shirin aurenta da zai gudana a watan Oktoba, ta mutu sakamakon hadarin motan.
'Yar uwar magayiyar, Magdalene Okuchu, ta bayyana sakon jimaminta a shafinta na Facebook.
Tace: "Har yanzu na kasa yarda, yan awanni kina magana cikin farin ciki, har kika daura kayayyakinki a kafar sada zumunta. Da Allah ya hanaki zuwa aiki yau da baki fuskanci hadarin ba."
KU KARANTA: Rabuwan kai tsakanin kabilar Igbo: Biyafara muke so, babu ruwanmu da kujeran shugaban kasa - Dattawan Biyafara
Tuni masu ta'azziya sun cika shafinta na Facebbok da sakonni.
Immaculate Okochu yar asalin Ebu a jihar Delta ce , kuma tana zama a Apapa, jihar Legas kafin mutuwarta.
Ta halarci makarantar sakandaren Ajeromi Ifelodun Senior High School da Kwalejin fasahar Yabatech.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng