Jagora a APC Ya Kalubalanci ‘Yan Majalisa a Kawo Hukuncin Kashe Barayin Gwamnati
- Majalisar dattawa ta kama hanyar kawo kudirin kashe wadanda aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi a Najeriya
- Injiniya Muazu Magaji ya bukaci sanatoci su waiwayi barayin gwamnati da kuma masu yiwa tattalin arziki zagon kasa
- ‘Dan siyasar yana so sanatoci su kawo doka a majalisar dattawa da za ta aika duk wanda ya saci dukiyar kasa zuwa barzahu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Majalisar dattawa ta na kokarin kawo wani kudiri wanda zai iya ganin bayan masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
Idan kudirin ‘yan majalisar ya kai matakin karshe, kuma ya samu sa hannun shugaban kasa, za a kashe masu harkar kwaya.
Dan-Sarauniya yana so a kashe barayin gwamnati
Yayin da ake tattanawa game da wannan yunkuri da sanatocin suka fito da shi, sai aka ji Muazu Magaji ya yi magana a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Injiniya Muazu Magaji wanda yana cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kano, ya bukaci majalisa ta waiwayi masu taba baitul-mali.
Majalisar dattawa da barayin gwamnati
‘Dan siyasar yana so sanatocin kasar su fito da kudirin da zai haifar da dokar da za ta halatta kashe wanda ya ci kudin mutane a gwamnati.
A rubutun da ya yi a shafinsa, ‘Dan sarauniya yana so majalisar dattawa ta yaki barayin gwamnati da masu yi wa tattali zagon-kasa.
Ana son kawo doka kan barayin gwamnati
“Senate (majalisar dattawa) sun sa dokar kisa kan masu fataucin miyagun kwayoyi masu sa maye da jirkita hankali!”
“Saura ta masu gurgunta tattalin arzikin kasa ta hanyar sata da kwashe dukiyar baitilmali tare da makarkashiya ga tattalin arziki.”
- Muazu Magaji
Majalisa za ta yaki barayin gwamnati?
Tuni dai jama’a su ka fara maida martani, aka samu wasu suna goyon bayan zancen, wasu kuma suna ganin abin da kamar wuya.
Wasu masu bibiyar tsohon ‘dan takaran gwamnan a Facebook sun ce idan majalisa tayi hakan, dokar za ta fara ne da ire-irensu.
Biyan giratutin tsofaffin ma'aikata a Kano
Kafin nan Legit Hausa ta ci karo da rubutun Dan sarauniya, inda ya tofa albarkacin bakinsa kan biyan giratuti da ake yi a jihar Kano.
A cewarsa, babu dalilin cika jama’a da surutu saboda za a biya tsofaffin ma’aikata kudin sallama, yake cewa dama hakkokinsu ne.
“Kano mun kai lalacewar da biyan hakkin Ma’aikata da yan fansho shine aiki da yin bajinta a gwabnati! Abinda shine Farrul - Ainihi!”
Idan za a tuna, gwamnatin baya ta gagara biyan ma’aikatan jihar Kano hakkokin na su.
Darajar kudin Najeriya, Naira ya fadi a duniya
A baya kun samu labari kima da darajar kudin Najeriya yana ta faduwa war-wasa bayan wani hobbasa da aka ji kwanakin baya.
Naira da kudin kasashen Zambiya da Ghana su ne a kashin baya, a kasuwar canji $1 ta kusa kai N1500 a lissafin yammacin Juma'a.
Asali: Legit.ng