Ganduje ya sake korar tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji, daga mukaminsa

Ganduje ya sake korar tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji, daga mukaminsa

  • A karo na biyu, Gwamna Ganduje na jihar Kano ya sallami Engr Mu'azu Magaji daga mukamin da ya bashi
  • Bayan tube sa daga kwamishina, Ganduje ya nada Dansarauniya matsayin shugaban kwamitin aikin iskar gas na jihar
  • A ranar Litinin, Gwamnan Kano ya bada sanarwar kwace mukamin saboda rashin kwazo tare da rashin biyayya

Kano - A karo na biyu a cikin shekara daya, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya, daga mukamin da ya nada shi.

Da farko, gwamnan ya sallami Magaji yayin da ya ke kwamishina bayan ya yi wata wallafar jin dadi kan mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu sakamakon cutar korona da yayi fama da ita.

Read also

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

A karo na 2, Ganduje ya fatattaki tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji daga mukaminsa
A karo na 2, Ganduje ya fatattaki tsohon kwamishinansa, Mu'az Magaji daga mukaminsa. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Amma kuma, bayan watanni kadan, Ganduje ya sake bai wa Magaji wani mukami, Daily Trust ta ruwaito.

An nada shi a matsayin shugaban aikin bututun iskar gas da kuma kwamitin masana'atun na jihar Kano.

Amma a ranar Litinin, Ganduje ya sawwake wa Magaji mukaminsa kan abinda ya kwatanta da "rashin kwazo da kuma rashin biyayya".

Kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar kuma Advice TV Nig ta wallafa a shafin ta na Facebook.

Takardar ta ce tsohon kwamishinan ya gaza kan abinda a ke bukatar ya yi na sauke nauyin nadin da aka masa kan aikin.

Kamar yadda takardar tace, shugabancinsa ga kwamitin wanda ke daya daga cikin abubuwan da ake bukata, shi ne ya kasance ya tabbatar da cewa an yi aikin a kan lokaci sai dai bai yi hakan.

Read also

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Takardar ta ce gwamnan ya umarci Magaji da ya mika ragamar kwamitin ga mataimakin shugaban kwamitin, Aminu Babba Dan'Agundi, wanda shi ne Sarkin Dawaki Babba na Kano.

Ganduje ya sake kai wa Rimingado 'farmaki', 'yan sanda na shirya sabbin tuhuma

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar na cigaba da kokarin mika sabbin tuhuma ga dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, kan zarginsa da ake da mika bayanan bogi gaban majalisar jihar Kano.

Idan za mu tuna, majalisar Kano ta gayyaci Rimingado domin ya bayyana a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar bayan korafin da aka mika gaban ta a ranar 14 ga watan Yuli.

Amma yayin dogaro da halin rashin lafiya tare da hadawa da takarda, Rimingado ya bukaci asalin kwafin korafin da aka mika gaban majalisar tare da bukatar karin lokaci kafin ya bayyana.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel