Majalisar Wakilai ta Umarci CBN ya Dakatar da Karbar Harajin Tsaron Yanar Gizo
- Majalisar wakilan Najeriya ta umarci babban bankin kasa da ya dakatar da aiwatar da harajin 0.5 % na tsaro ta yanar gizo da aka kakabawa 'yan kasar nan
- Umarnin na zuwa ne bayan kudirin gaggawa da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya gabatar a yau Alhamis a zauren majalisa
- Sanarwar da babban bankin na CBN ya fitar a ranar Litinin ta ce za a fara aiwatar da harajin cikin mako 2 bayan fitar da sanarwar, wanda tuni batun ya yamutsa hazo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Majalisar wakilai ta umarci babban bankin kasa da ya dakatar da aiwatar da harajin 0.5 % na tsaro ta yanar gizo kan hada-hadar kudi.
Wannan ya biyo bayan kudirin gaggawa da shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya gabatar a yau Alhamis.
Sanarwar da babban bankin na CBN ya fitar a ranar Litinin ta ce za a fara aiwatar da harajin ne mako biyu daga ranar da aka sanar da shi, kamar yadda Premium Times ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta ce harajin tsaron gizo kuskure ne
Tun bayan sanar da harajin da bankin CBN ya yi, ‘yan Najeriya, ciki har da kungiyar dattawan Arewacin kasar nan ke bayyana rashin dacewar hakan saboda matsin da ake ciki.
A zamanta na yau, majalisar wakilai ta dubi koken yan Najeriya, inda ta bayyana matakin sanya harajin ta yanar gizo a matsayin kuskure, kamar yadda Intel region ta wallafa.
Tun da fari, babban bankin kasa CBN ya umarci bankuna su fara cirar kudin tsaron intanet mako biyu bayan bayar da umarnin, wanda ya ce ya yi daidai da gyaran da aka yi wa dokar tsaro ta internet ta 2024.
Da yake jagorantar muhawarar kan kudirin, Mista Chinda ya ce CBN ya aiwatar da dokar ta yanar gizo bisa kuskure.
Majalisar ta umurci CBN da ya janye wannan matakin mai cike da rudani.
Shehu Sani ya fadi dalilin sa haraji
Kun ji a baya cewa tsohon Sanata, Shehu Sani ya ce karambanin ‘yan Najeriya ne ya sanya gwamnatin tarayya kakaba musu haraji.
Ya bayyana hakan ne a wani salo na shagube yayin da Najeriya ta dauki dumi kan batun karin harajin tsaro da babban bankin kasa CBN ya ayyana.
Asali: Legit.ng