"Daukar Fetur a Jarka zai Iya Babbake Fasinjoji," FRSC ta Gargadi Masu Abubuwan Hawa
- Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa kan daukar fetur a cikin jarkoki idan suna tafiya domin gujewa asarar rayuka
- Ana zargin wasu masu ababen hawa, musamman na haya da dura man fetur a jarka suna guzurinsa gudun kada ya kare a hanya kuma babu mai a kusa
- Shugaban hukumar a jihar Kogi, Mista Samuel Oyedeji ya ce ba karamar kasada ba ce daukar fetur a jarka domin za ta iya haddasa gobarar da za ta kashe fasinjoji
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kogi - Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ta gargadi masu ababen hawa kan daukar fetur a cikin jarkoki idan suna tafiya.
Hukumar ta ce bijirewa shawarar ka iya jawo mummunan gobara wanda zai iya jawo asarar rayukan fashinjojin da ake dauke da su.
FRSC ta halarci taron WARSO
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, shugaban hukumar a jihar Kogi, Mista Samuel Oyedeji ne ya yi jan kunnen a wani taron ranar kungiyar Afrika ta Yamma kan tsaro a hanyoyi (WARSO).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da karanci da kuma tsadar man fetur, inda ake zargin masu motocin hayar ke dura fetur a jarka domin gudun kada ya kare musu a hanya.
FRSC: "Hadarin daukar fetur a jarka"
Mista Samuel Oyedeji, shugaban hukumar kare afkuwar hadurra a hanyoyin kasar nan reshen jihar Kogi, ya ce akwai hatsari sosai a tattare da daukar mai a jarka.
Jami'in ya ce lamarin ka iya yin muni ga masu ababaen hawa, domin za ta iya jawo gobara ana tsaka da tafiya a hanya, kamar yadda PM News ta tatataro.
Mista Samuel Oyedaju ya bayyana cewa irin wannan hatsarin ka iya jawo rasa rayuka da dama a kan hanyoyin kasar nan.
Ya ba masu ababen hawa shawarar su kaucewa daukar fetur a jarka suna tafiya da shi domin a tsira da rai da lafiya.
“FRSC za ta iya kwace motoci,” Kotu
A baya mun kawo muku labarin cewa wata kotu ta jaddada ikon da hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa (FRSC) ke da shi wajen kwace ababen hawan da suka karya doka.
Hukuncin ya biyo bayan karar da wani lauya ya shigar kan cin tararsa da FRSC ta yi bayan kama shi yana tuka mota ba tare da lasisi ba da rashin kwayun taya.
Asali: Legit.ng