" Za a Gama Titin Abuja Zuwa Kaduna Zuwa Katsina" Ministan Tinubu Ya Tsaida Lokaci
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kammala aikin gina titin Abuja-Kaduna-Kano-Katsina nan da karshen shekarar 2025
- Ministan ayyuka, David Umahi wanda ya bayyana hakan ya ce kamfanin Dangote, BUA da Julius Berger ne za su yi aikin
- Umahi ya ba da tabbacin kammala aikin titin Sokoto zuwa Badagry a kan lokaci wanda zai hada Kudu maso Gabas da Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan ayyuka David Umahi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin kammala aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano-Katsina nan da shekarar 2025.
David Umahi ya ce shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya samar da wani tsari da zai taimaka wajen kammala aikin titin a shekara mai zuwa.
Yadda za a gina titin Abuja-Katsina
Jaridar The Punch ta ruwaito Umahi, a wata ziyara da gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya kai masa, ya yi bayani kan dabarun da ake aiwatarwa domin kammala aikin titin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Uchenna Orji, ministan ya ce:
“Za a fara kammala kashi na farko na titin mai tsayi kilomita 76, wanda rukunin kamfanoni na Dangote ke aikin wanda zai gina shi da kankare.
"Za mu ba da izinin gina kilomita 82 na gaba ga kamfanin Julius Berger. Sannan kuma kamfanin BUA zai yi aikin kilomita 40 na ƙarshe wanda shi ma za a yi shi da kankare."
Gwamnati ta himmatu kan titin Sokoto-Badagry
Ministan ya kuma jaddada kudirin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da aikin titin Sokoto zuwa Badagry cikin gaggawa tare da kammala shi a kan lokaci, jaridar Tribune ta ruwaito.
"Ma'aikatar ayyuka ta tarayya ce ke gudanar da aikin gina babbar hanyar kuma aikin zai shafi tsohuwar hanyar kasuwanci ta Afirka da ta bi ta Sokoto, Kebbi, Niger, Kwara, Ondo, Oyo, Ogun, Legas, ta kuma hade da Badagry."
- David Umahi
Ya ce ana shirin hada Kudu maso Gabas da Arewa ta hanyar gina titin kasuwancin wanda zai bi ta jihohin Binuwai, Kogi, Nasarawa, da kuma Abuja.
Gwamnati za ta kara harajin VAT
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta ce akwai bukatar ta kara harajin VAT da take caja yayin da aka sayi kaya ko aka sayar.
Kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji ya kawo wannan shawar yana mai cewa hakan zai bunkasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng