Kamfanin Microsoft Zai Tattara Kayansa Ya Bar Najeriya, Mutane Za Su Rasa Ayyukan Yi
- Kamfanin Microsoft ya fara shirye-shiryen rufe cibiyar bunkasa Afrika (ADC) da ya bude a Najeriya, wadda ke a Ikoyi, jihar Legas
- Ba tare da bayar da wani dalili ba, an gano cewa, a ranar Litinin Microsoft a ranar ya sanarwa ma'aikatansa cewa zai rufe cibiyar
- Da wannan mataki na rufe cibiyar, ana fargabar akalla ma'aikata 200 ne za su rasa ayyukansu, duk da cewa za su karbi albashin Yuni
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Lagos - Babban kamfanin kimiya na kasar Amurka, Microsoft, ya fara shirye-shiryen rufe daya daga cikin ayyukansa da aka fi sani da cibiyar bunkasa Afrika (ADC), wadda ke a Legas.
Cibiyar ADC ta Microsoft na nan Ikoyi, babban birnin jihar Legas, hedikwatar kasuwanci ta Najeriya, kuma mafi girman tattalin arziki a Afrika.
Microsoft zai biya ma'aikata albashin Yuni
Ba tare da bayar da wani dalili ba, an gano cewa, kamfanin Microsoft a ranar Litinin ya sanarwa ma'aikatansa cewa zai rufe cibiyar ADC ta Legas, The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma gano cewa kamfanin zai biya ma'aikata albashi har zuwa Yuni tare da kuma biyan kudaden inshorar lafiyarsu.
Yayin da ma'aikata ke ci gaba da alhinin abin da ke shirin faruwa da su, rahoton jaridar Vanguard ya alakanta rufe cibiyar Microsoft da tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.
A cewar rahoton, Microsoft zai rufe ofishinsa na Yammacin Afrika da ke Najeriya, amma ba zai rufe ta Gabashin Afrika da ke Nairobi, Kenya ba.
Ma'aikata 200 za su rasa aiki a Microsoft
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa a shekarar 2019, kamfanin Microsoft ya kashe Dala miliyan 100 domin bude cibiyoyin ADC a Najeriya da Kenya.
A cibiyarsa ta Najeriya, ya fara daukar injiniyoyi 120 aiki a shekarar 2022, inda ya ci gaba da kara yawansu har suka kai sama da ma'aikata 200 a halin yanzu.
Da wannan mataki na barin Najeriya, ana fargabar akalla ma'aikata 200 ne za su rasa ayyukansu, yayin da kasar ke kara fama da yawan marasa ayyukan yi.
Gwamnati za ta sayar da rijiyoyin mai
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta sanar da shirin sayar da akalla rijiyoyin mai 17 a yayin da za a sabunta lasisin rijiyoyin a 2024.
Karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce wannan karon ba za a sayar da rijiyoyin ga 'yan siyasa ba domin dawo da martabar rijiyoyin.
Asali: Legit.ng