Mun Gaji Da Lamarin Kasar Nan: Jerin Shahrarrun Kamfanoni 12 Da Suka Bar Najeriya

Mun Gaji Da Lamarin Kasar Nan: Jerin Shahrarrun Kamfanoni 12 Da Suka Bar Najeriya

 • Manyan kamfanonin kasashen waje dake aiki a Najeriya sun sayar da dukiyarsu ga yan kasar
 • Kamfanonin sun fita daga Najeriya bayan kwashe shekaru wajen baiwa dubunnan yan Najeriya aiki
 • Shugabannin wadannan kamfanoni sun bayyana dalilansu inda suka ce ba zasu taba dawowa ba

Wasu kamfanoni sun tattara inasu-inasu sun bar Najeriya a kwanakin nan bisa dimbin dalilai da suka bayar.

Kamfanonin sun hada masu kere-kere, kasuwanni, da na man fetur.

Daya daga cikin kamfanonin mai suna 'The Game' ya kwashe kayansa a 2022 bayan shekaru 17 yana aiki a Najeriya.

Etisalat
Mun Gaji Da Lamarin Kasar Nan: Jerin Shahrarrun Kamfanoni 12 Da Suka Bar Najeriya
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamfanin 'The Game' mallakin Massmart Holdings Limited ya shiga jerin su Shoprite, HSBC, da Etisalat da sauran su da suka sayar da dukiyoyinsu ga masu zuba jari.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP 10 da Suka Tserewa Harin Boko Haram Sun Tuba, Sun Ajiye Makamansu

Legit ta tattaro muku jerin wadannan kamfanoni da suka bar Najeriya:

 1. Truworths
 2. Etisalat
 3. ExxonMobil
 4. Tiger Brands
 5. HSBC and UBS
 6. Mr Price Group Ltd
 7. Woolworths
 8. Shoprite
 9. Game
 10. Brunel Services plc
 11. Iberia Airline
 12. InterContinental Hotel Group

Dalilan fitarsu daga Najeriya

Jaridar BusinessDay ta ruwaito wasu dalilai da ke sa kamfanonin barin Najeriya amma babba ciki shine matsalar canjin kudi da darajar Naira.

Mafi akasarin kamfanoni na fuskantar matsala wajen samun Dalar Amurka da sauran kudaden kasashen waje don sayo kayayyaki.

Abin ya tsananta inda bayan samun arziki a Najeriya, suna fuskantar kalubale wajen mayar da dukiyoyin kasashensu.

Shugabannin kamfanonin sun yi magana

Jawabi kan dalilin arcewarsu daga Najeriya, shugaban rukunin kamfanonin Massmart (mamallakan Game Stores), Mitch Slape, ya bayyana cewa:

"Wahalar gudanar da harkar kasuwanci a Najeriya abune wanda ake bukatar gyara gaskiya."
"Da 'dan sauki idan kuna fadi amma kwastmominku na karuwa ko kuma dan karamin koma baya ne. Amma a lamarinmu, abin ya wuce koma baya, muna samun riba sai kuma lokaci guda abubuwa suka dagule."

Kara karanta wannan

Kwararan Dalilai 5 Dake Nuna Cewa Wajibi CBN Ya Dage Ranar Daina Amfani da Tsaffin Takardun Naira

Shugaban kamfanin Mr Price, Mark Blair, shi kuma a jawabinsa ya bayyana cewa ba zai sake zuba kudinsa a Najeriya ba.

Reuters ta ruwaito Mark Blair da cewa:

"Maganar gaskiya itace ban shirye sake zuba kudi na a kasar nan ko kasa mai matsala irin wannan ba."
"Da farko muna samun kudi, amma yanzu matsalolin sun yi yawa ne rututu, ko fitar da kudi ya gagara."

Asali: Legit.ng

Online view pixel