Timipre Sylva: NNPC sun hako rijiyoyin danyen mai biyu a jihar Gombe

Timipre Sylva: NNPC sun hako rijiyoyin danyen mai biyu a jihar Gombe

- Gwamnatin tarayya ta na yunkurin nemo mai a yankin Arewacin Najeriya

- Ministan man fetur, Timipre Sylva ya bayyana irin nasarorin da ake samu

- Timipre Sylva ya ce an gano wasu rijiyoyi a Gombe a aikin da NNPC yake yi

Karamin ministan harkokin mai na kasa, Timipre Sylva, ya ce an yi nasara a yunkurin neman danyen mai da NNPC ya ke yi a Arewa maso gabas.

Jaridar Punch ta ce Mista Timipre Sylva ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba.

Ministan tarayyan ya ke cewa an hako rijiyoyi biyu na danyen mai a jihar Gombe, yayin da NNPC ke cigaba da laluben danyen mai yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: Najeriya ta samu fiye da $200bn daga man fetur a shekara 5- OPEC

Da aka nemi Timipre Sylva ya yi bayani a game da inda aka kwana a aikin neman mai, sai ya ce: “Shakka babu mun tsunduma sosai a wannan aikin.”

“Mun riga mun samo mai. Mun hako rijiyoyi biyu yanzu a Arewa maso gabas, a yankin Gombe, an yi nasara, kuma za a cigaba da aiki a yankin Chadi.”

Sylva ya bayyana cewa gwamnatinsu ta karkashin NNPC za ta cigaba da wannan gagarumin aiki.

A na ta bangaren, gwamnatin jihar Gombe za ta bada goyon bayan domin ganin NNPC ya cigaba da laluben danyen mai har zuwa yankin kasar Gongola.

KU KARANTA: Farashin litar man fetur ya kara tashi

Timipre Sylva: NNPC sun hako rijiyoyin danyen mai biyu a jihar Gombe
Neman danyen mai a Arewa Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta ce duka al’ummomin jihohin da ake wannan aiki, a shirye suke da su bada gudumuwarsu wajen ganin NNPC ya hako danyen mai.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen ganin an samu mai a wajen Neja-Delta.

A baya kun ji cewa an gano arzikin man fetur mai dimbin yawa a jihar Benue, kuma masana ilimin ma'adinan Najeriya ke jagorantan wannan bincike.

Najeriya ta na harin ajiyar danyen mai akalla ganguna milyan 40 domin a rika kai wa ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel