Labari mai dadi: NNPC zata soma hako mai a rijiyoyin mai 4 a Arewa
Rukunin kamfanin nan dake kula da albarkatun man fetur na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a takaice ya sanar da aniyar sa ta fara aikin hako mai daga rijiyoyin mai akalla takwas a yankin Gongola dake a arewacin Najeriya a cikin shekarar nan ta 2018.
Wuraren da rijiyoyin man suke kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu sun hada da Kolmani River-1, Nasara-1 da kuma Kuzari-1.
KU KARANTA: Sarkin musulmi ya ce Buhari bacci ya ke
Legit.ng ta samu cewa kamfanin na NNPC ya bayyana cewa ya yanke wannan hukuncin ne na karkatar da akalar aikin sa ya zuwa yankin na Gongola biyo bayan tsaikon da aka samu na sace wasu masu binciken man a yankin gurbin tafkin Chadi.
A wani labarin kuma, Mun samu cewa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin tsohon mataimakin gwamnan jihar Filato, Mista Ignatius Longjam a matsayin wanda zai maye gurbin Marigayi Birgidiya Janar John Shagaya a matsayin shugaban hukumar nan ta koyar da tsare-tsare da ke Kuru.
Mun samu dai cewa kafin mutuwar sa a ranar 11 ga watan Fabrerun da ta gabata, Janar John Shagaya shine shugaban ukumar nan ta koyar da tsare-tsare da ke Kuru watau National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) Kuru.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng