Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Tafiyar Tinubu da Aka Ce Ya Ɓata Kafin Ya Dawo

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Tafiyar Tinubu da Aka Ce Ya Ɓata Kafin Ya Dawo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, 2024 fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki ƙasar Netherlands kuma zai wuce Saudiyya.

Sai dai sama da mako ɗaya da kammala taron da Shugaban Ƙasa Tinubu ya halarta a Saudiyya, ba a sake jin ɗuriyarsa ba kuma fadar shugaban kasa ta yi gum.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Kwanaki sama da 7 Bola Tinubu bai dawo gida ba bayan kammala taron WEF a Riyadh Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku yadɗa tafiyar Bola Tinubu ta kasance zuwa Netherlands da Saudiyya kuma jinkirin dawowarsa gida Najeriya.

Ziyarar aikin Tinbubu zuwa Netherlands

A sanarwar da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya wallafa a shafin X, ya ce Tinubu zai je ƙasar Holland ne bisa gayyatar da Firaministan ƙasar, Mark Rutte, ya aiko masa.

Kara karanta wannan

Jirgin shugaba Tinubu ya iso Najeriya bayan kwashe makonni a kasashen waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tsare-tsaren zamansa a Netherlands, Ngelale ya ce Shugaba Tinubu zai gana da Firaministan ƙasar sannan zai tattauna da Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima.

Yayin ganawarsa da Firaministan Holland a gidansa ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, Shugaba Tinubu ya jawo hankalin masu zuba hannun jari su taho Najeriya

Tinubu ya ce akwai damarmaki masu yawa a ɓangarori daban-daban a Najeriya kuma gwamnatinsa a shirye take ta buɗe hanyoyin zuba jari.

Tinubu ya wuce taron WEF a Riyadh

Bayan kammala ziyara a Holland, Bola Tinubu ya zarce zuwa birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya domim halartar taron tattalin arzikim duniya (WEF).

A wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin midiya, Olusegun Dada, ya ce taron ya gudana ne ranar 28 da 29 ga watan Afrilu.

Tinubu ya bi sahun takwarorinsa shugabannin ƙasashe da dama wajen halartar tattaunawa kan muhimman batutuwa a taron tattalim arzikin da ya gudana a Saudi.

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Bayan haka kuma shugaban ƙasar ya gana da attajirin nan, Bill Gates, mamallakin Microsoft ranar Lahadi a birnin Riyadh.

Yayin wannan zama, Tinubu ya faɗawa fitaccen attajirin cewa fasahar zamani da cin hanci ba su shiri da juna kuma gwamnatinsa ta shirya bunƙasa fasaha don kawo ƙarshen cin hanci.

A wata sanarwa da hadiminsa ya fitar, shugaban ƙasar ya ce:

"Fasaha tamkar makiyi ce ga zamba, cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya, mun fara aiki tuƙuru domin inganta fasahar mu."

Ina Tinubu ya shiga bayan taron Saudiyya?

Bayan kammala taron Saudi Arabia ranar 29 ga watan Afrilu, ba a sake jin motsin shugaban ƙasa ba wanda aka yi tsammanin zai kamo hanya zuwa Abuja.

Sama mako ɗaya bayan taron, babu Tinubu babu labarinsa kuma fadar shugaban ƙasa ta yi shiru ba ta ce komai ba game da ƙasar da shugaban ya zarce.

Bayan wani ɗan lokaci, an fara jita-jitar wataƙila Shugaba Tinubu ya wuce ƙasar Faransa ne inda galibi yake zuwa domin ganin likitocinsa a Faris.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana lokacin dawowar Tinubu gida Najeriya

Duk da babu wata sanarwa a hukumance kan inda Bola Tinubu ya shiga, wata majiya a fadar shugaban ƙasa ta yi iƙirarin cewa yana can birnin Landan.

A rahoton da muka kawo maku, majiyar ta ce Tinubu ya zarce birnin Landan ne a wata ziyara ta ƙashin kansa wadda ba ta da alaƙa da aikin ofishinsa.

Yaushe Bola Tinubu zai dawo Najeriya?

Ana haka ne aka samu labari daga fadar shugaban ƙasa cewa Mai girma Tinubu zai dawo gida Najeriya ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, 2024.

Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai ne ya bayyana haƙa a shafinsa na manhajar X.

Sai dai bai faɗi ƙasar da Tinubu yake ba yanzu haka, ya dai ce shugaban ƙasar da tawagarsa za su kamo hanyar gida daga nahiyar Turai.

Shettima ya fasa zuwa Amurka

A wani rahoton kuma Kashim Shettima ya fasa tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a taron kuwanci a Dallas.

Mataimakin shugaban ƙasar ya soke wannan tafiya ne sakamakon wata tangarɗa da jirginsa ya samu, ministan waje zai wakilci Tinubu a taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262