Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga ’Yan Fashi a Jihar Ekiti

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Ga ’Yan Fashi a Jihar Ekiti

  • Alkalin babbar kotun jihar Ekiti, mai shari'a Lekan Ogunmoye, ya yanke wa wasu 'yan fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Mai shari'a Ogunmoye ya ce an kama mutanen da laifi kafun yanke musu hukuncin kuma yana fata hakan ya zama izina ga 'yan baya
  • Kotun ta kuma bayyana irin laifuffukan da suka aikata wurin keta alfarmar al'ummar da suke yiwa fashin da makamin a fadin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ekiti - Babbar kotun jihar Ekiti da ke Ado Ekiti ta yanke wa wasu 'yan fashi da makami uku hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Police IG
Kotu za ta rataye 'yan fashi da makami a jihar Ekiti. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

An kama mutane da fashi da makami

Kara karanta wannan

Kotu ta saka ranar cigaba da sauraron shari'ar Abduljabbar Kabara a Kano

'Yan fashi da makamin su uku sun hada da Oyebanji Sola, Jiomoh Azeez da kuma Ogunlade Babatunde.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, kotun ta yanke wa Babalola Bidemi hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali yayin da ta wanke Akinwale Oluwaseun.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an fara gurfanar da mutanen ne tun ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 a gaban mai shari'a Lekan Ogunmoye.

Laifukan da aka zarge su da aikatawa

Ana zarginsu ne da aikata laifuka guda biyar da suka hada da hadin baki, fashi da makami, ajiyar kayan sata da shiga kungiyar asiri.

Kotun ta tabbatar da cewa mutanen sun yi fashin talabijin din bango, agogon hannu, riguna da wanduna da kudi N5,000 da sauransu ga wasu mutume guda biyu; Tijani Omowumi da Ogunrinde Olumide.

A lokacin da suka yi fashin suna dauke da sanda, adduna da bindiga wanda hakan laifi ne a dokar kasa, cewar the Guardian.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

Wadanda suka yiwa fashi sun magantu

Daya daga cikin wadanda suka yi wa fashin ta labarta cewa sun shigo dakinta ne da misalin karfe 10.00 na dare suna rike da makamai.

Ta kara da cewa wani daga cikinsu ya yi niyyar mata fyade sai sai daya daga cikin 'yan fashin ya hanasa.

Alkalin kotun, mai shari'a Lekan Ogunmoye ya ce ya yanke musu hukuncin ne domin hakan ya zama izina ga 'yan baya.

Kotu ta yanke hukunci kan zaben Kano

A wani rahoton, kun ji cewa a zaman da ta yi na sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna.

A hukuncin da Kotun ta yanke, ta tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP shi ne halastaccen gwamnan Kano ta kuma ce akwai kurakurai a hukuncin da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng