Rashin tsaro: 'Yan fashi za su dandana kudarsu yayin da IGP ya tura dakaru na musamman 302 zuwa jihar Kaduna

Rashin tsaro: 'Yan fashi za su dandana kudarsu yayin da IGP ya tura dakaru na musamman 302 zuwa jihar Kaduna

- Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta mayar da martani a kan yawan tashe-tashen hankulan da‘ yan fashi ke haddasawa a jihar Kaduna

- Don dakilewa da kawo karshen wannan mummunan al'amari, IGP Mohammed Adamu ya tura jami'ai daga bangarori daban-daban zuwa yankunan da ke fama da rikicin

- Shugaban rundunar ‘yan sanda ya bukaci dakaru a karkashin Operation Puff Adder da su kai yakin har zuwa kofar 'yan fashin

A wani kokari da ake na shawo kan matsalar fashi da makami, satar mutane, da sauran laifuka masu nasaba da hakan a Kaduna, Sufeto-Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya tura akalla dakarun tsaro na Musamman guda 302 zuwa jihar.

A cewar IGP Adamu, babban manufar wannan runduna ita ce kwato sarari daga hannun masu aikata laifuka wadanda ke barazana ga lamarin tsaron cikin gida.

KU KARANTA KUMA: Daliban Kagara: Ba 'yan fashi bane - Tsoro ya mamaye Neja yayin da sanata ya bayyana asalin masu satar mutane

A cewar gidan talabijin din Channels TV, za a tura rundunar tsaro na musamman wadanda suka hada da mambobi daga sashin yaki da ta'addanci, rundunar tafi da gidanka, da kuma runduna ta musamman na 'yan sandan Najeriya zuwa yankunan da ake rikici.

Shugaban 'yan sandan da yake magana a kan' Operation Puff Adder 'gabanin tura su, ya umarci dakarun da su kai yaki har zuwa kofar 'yan fashin sannan kuma su dawo da zaman lafiya a wuraren da ake rikici.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun kai hari a kauyen Baka, karamar hukumar Igabi da ke Kaduna, inda suka kashe uba da dansa a safiyar ranar Asabar, 13 ga Fabrairu.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, ya tabbatar da ci gaban.

KU KARANTA KUMA: Satar Kagara: Gwamnan Neja ya gana da Buhari, ya yi karin haske a kan ceto su

Kwamishinan ya ce 'yan fashin sun yi ta harbi ba kakkautawa sannan suka shiga gidan mamacin wanda ya kasance manomi a yankin ta karfin tuwo.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng