'Yan sanda sun fatattaki wasu 'yan fashi da makami a Abuja
- Hukumar 'yan sandan babban birnin tarayya ta ce ta mayar da harin da 'yan fashi 3 suka kai Gwarimpa dake Abuja
- Al'amarin ya faru ne a ranar Talata kamar yadda ASP Mariam Yusuf, jami'ar hulda da jama'an 'yan sandan ta tabbatar
- Yusuf ta bayyana yadda aka kashe 'yan fashin guda biyu lokacin da suka yi kokarin tserewa da ababen da ya sato
Hukumar 'yan sandan Abuja ta ce ta mayar da harin da wasu 'yan fashi 4 suka kai wa wasu mutane a wurin Gwarimpa dake Abuja.
ASP Mariam Yusuf, jami'in hulda da jama'an Abuja ta bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Talata.
Yusuf ta bayyana yadda lamarin ta faru da safiyar Talata a 7th Avenue, Gwarimpa Estate dake Abuja, Vanguard ta wallafa.
KU KARANTA: Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa
Ta bayyana yadda suka samu nasarar kashe biyu daga cikin 'yan fashin suna kokarin tserewa da abubuwan da suka sata, sauran kuma suka tsere.
Ta kara da bayyana yadda suka kwace abubuwan da suka sata wadanda suka hada da abubuwan na'ura mai kwakwalwa, wayoyi da kudade masu dumbin yawa.
Har wa yau ta bayyana yadda 'yan fashin suka kai hari Apo-Dutse, wuraren Apo, inda suka yi sace-sace.
Yusuf ta ce 'yan fashin sun harbi mazauna wurin inda suka harbi wani jami'in tsaro wanda yanzu haka yake asibiti ana kulawa da lafiyarsa.
Tuni 'yan sanda suka fara zagayen yawo wurin nemo 'yan fashin da suke yawo a gari. PPRO ya kara tabbatar wa da jama'a cewa za su tsaya tsayin-daka wurin kulawa da rayuka da dukiyoyin al'umma.
KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce
A wani labari na daban, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC da ake yi a jihar Kwara.
A wani taron manema labarai a garinsu na Oro, Mohammed a ranar Litinin ya ce jami'an da aka tura jihar domin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar da yi wa marasa rijistar sun yi karantsaye ga dokokin da aka gindaya musu.
Ya ce kwamitin sun taka dokar da aka gindaya wurin rarrabe kayan aikin, Premium Times ta ruwaito.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng