Amurka da Faransa Za Su Kafa Sansanin Sojoji a Najeriya? Gwamnati Ta Yi Karin Haske

Amurka da Faransa Za Su Kafa Sansanin Sojoji a Najeriya? Gwamnati Ta Yi Karin Haske

  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya wanke gwamnatin tarayya kan zargin za a kafa sansanonin sojojin kasashen waje a kasar
  • Mohammed Idris, a sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ya ce labarin da ake yadawa kan kafa sansanonin karya ce kwai aka shirya
  • Ministan ya kuma jaddada cewa Najeriya ta riga ta samu duk wani taimako daga kasashen waje da take bukata wajen samar da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ba gaskiya ba ne cewa ana tattaunawa tsakanin Najeriya da wasu kasashen ketare kan batun kafa sansanonin sojojin kasashen waje a kasar.

Gwamnatin ta yi martani ne kan jita-jitar da ta mamaye kafofin sada zumunta na zargin cewa tana tattaunawa da wasu kasashen ketare kan maido da sansanonin sojojinsu zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Kungiyar NECA ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan karin albashin ma'aikata

Gwamnati ta yi magana kan kafa sansanin sojojin kasashen waje a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta karyata zargin shirin kafa sansanonin sojin Amurka da Faransa a kasar. Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da "wannan karyar".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin Tarayya ba ta yi ba ko kuma fara irin wannan tattaunawar da wata kasar waje ba."

Gwamnati ta wanke kanta kan 'jawo' sojoji

Idris, a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce gwamnatin tarayya ba ta samu wata bukata ko yin wata shawara ta kafa sansanonin sojan kasashen waje a kasar ba.

"Gwamnatin Najeriya ta riga ta samu duk wani hadin guiwa daga kasashen waje da take bukata wajen tunkarar kalubalen tsaro.
"Shugaban kasar na ci gaba da jajircewa wajen yaukaka wannan kawancen, da nufin cimma manufofin tsaron kasa na ajandar sabunta makomar Najeriya."

- A cewar sanarwar.

Sojojin waje: Manyan Arewa sun gargadi Tinubu

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta musanta shirin korar wadanda Ganduje ya dauka aiki

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, wasu shugabannin Arewa sun gargadi Shugaba Tinubu kan barin Amurka da Faransa su mayar da sansanonin sojinsu daga yankin Sahel zuwa Najeriya.

A cikin wata wasika da suka aikawa Tinubu da ‘yan majalisar tarayya a ranar Juma’a, shugabannin Arewa sun ce amincewa da kafa sansanonin zai zamo hadari ga kasar nan.

Shugabannin arewacin kasar sun ce ana zargin Amurka da Faransa suna zawarcin Najeriya, da sauran kasashen yankin, domin sanya hannu kan wasu sabbin yarjejeniyoyin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.