'Yan Arewa Sun Yi Barazanar Daina Kai Kaya Kudu Saboda Jawo Masu Asara da Tsageru Ke Yi
- Dillalai masu kai kaya Kudu sun bayyana aniyarsu ta yiwuwar rage kai kaya Kudancin Najeriya saboda bata masu harka
- Shugabannin kungiyar dillalan tumatur sun zargi jawo masu asara a wata husumar da ta barke a wata kasuwa a jihar Legas
- Akan samu hargitsi a jihohin Kudu a lokuta mabambanta, kuma akan jawo asara ga ‘yan kasuwa daga Arewacin Najeriya
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Kaduna - Kungiyar dillalan tumatur ta Najeriya da hadaddiyar kungiyar dillalan kayan abinci da shanu ta Najeriya sun yi barazanar rage kai tumatur jihar Legas saboda lalata musu dukiya da ake.
Shugaban kungiyar dillalan tumatur na kasa, Alhaji Ahmed Alaramma ne ya yi wannan barazanar a taron manema labarai a Zara, jihar Kaduna a ranar Lahadi.
Ya ce lamarin da ya faru a kasuwar Oke-Odo da ke Legas, ya kai ga lalata kwandunan tumatur sama da 60,000 da babu kowa a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Area Boys’ ne suka aikata barna a kasuwa
Alaramma ya bayyana cewa, an fara amfani da kwandunan ne wajen kai tumatur zuwa Kudancin, rahoton Daily Trust.
A cewarsa:
“Sama da mambobin kungiyar 70 ne ke ba da hayar kwandunan ga dillalan tumatur a fadin kasar nan; muna da akwatuna sama da 60,000 da ake shirin mayar da su Arewa a kasuwa a lokacin da rikicin ya tashi.
“Wadannan ‘yan daba ne suka kona su a lokacin arangamar kuma dai yaran ne suka hana mutanenmu kashe gobarar. Muna da shaidun bidiyo da wasu shaidun da ke nuna hakan."
Asarar da aka jawowa ‘yan kasuwar Aewa
A cewarsa, kowane holokon kwando ya kai Naira 6000; don haka mambobin kungiyar sun yi asarar jarin sama da N360m, The Guardian ta ruwaito.
A lokuta mabambanta, akan jawowa ‘yan kasuwar Arewa da ke kai kaya Kudu asara miliyoyin kudi.
Wannan na jawo masu mummunar asarar da ke kai su ga dauke kafa da kai kaya yankin Kudancin kasar.
Yadda 'yan kasuwa suka shiga yajin aiki
A shekarar 2021 'yan kasuwar shanu suka shiga yajin aiki a jihar Legas bayan da suka yi kukan yadda aka jawo masu asara.
Sun bayyana cewa, a lokacin zanga-zangar ENDSARS, an kone kayayyaki daban-daban mallakin 'yan kasuwar shanu.
Ba sabon lamari bane a jawowa 'yan kasuwa asara a Kudu masu Yammacin Najeriya, musamman 'yan shanu da hatsi.
Asali: Legit.ng