Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu

Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu

- Kungiyar masu kai shanu da abinci kudu sun shiga yajin aikin da ba a san dawowarsu ba

- Kungiyar ta bayyana cewa. gwamnatin tarayya ta gagara sauraran kokensu balle a biya bukatarsu

- Hakazalika kungiyar ta gargadi dukkan masu kai kayan abinci da shanu kudu kan motsa kaya daga arewa zuwa kudu

Dillalan shanu da na Abinci a karkashin gamayyar dillalan kayan masarufi da shanu watau (AUFCDN), a yau za su fara yajin aiki a duk fadin kasar bayan karewar wa’adin kwanaki bakwai da ta ba gwamnatin tarayya don ta biya bukatunsu.

AUFCDN, wata memba a kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) a ranar Lahadi a wani taron manema labarai ta ce kungiyar na neman kariyar mambobinta, ta biya diyyar biliyan N475 na mambobin da kadarorin da suka yi asara yayin zanga-zangar #EndSARS da rikicin Shasa.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati da ta ba da umarnin rusa dukkan shingayen da ke kan titunan tarayya saboda matsalolin da mambobinta ke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa

Wata sabuwa: Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu
Wata sabuwa: Dillalan shanu da na kayan abinci sun shiga yajin aikin kai kaya Kudu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Babbar uwar kungiyar ta AUFCDN, Hajiya Hauwa Kabir Usman, a yayin da take bayar da bayani a lokacin da take zantawa da wakilinmu, ta gargadi ‘yan sanda da kada su hargitsa kungiyar da za su aiwatar da yajin aikin.

Yajin aikin zai kasance ta hanyar tabbatar da cewa ba wani abinci da shanu da aka motsa daga Arewa zuwa Kudu.

Hajiya Hauwa ta ce, “Tuni shugabannin kungiyar suka yi wani kwakkwaran shiri na tabbatar da cewa an rufe dukkan hanyoyinmu (kan iyakokinmu) tsakanin bangaren Arewa da na Kudu.

“Duk motar da zata fita sai an duba ta. Idan kun ɗauki wani nau'in abinci ko shanu, ba za ku iya fitar da shi ba, sai dai in ku komo da shi ko a lalata shi a can.

"Babu wani daga cikin jami'an tsaro da ya isa ya kuskura ya kusanci mambobin kwamitinmu domin idan suka yi hakan, za mu saba mishi bisa doka.”

Hajiya Hauwa ta sha alwashin cewa kungiyar ba za ta sassauta ba har sai gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu, tana mai cewa tun farko sun bayar da wa’adin kwanaki 21 ba tare da gwamnati ta mayar da martani ba.

KU KARANTA: Masu bukulun na sayi jirage har 3 sai sun mutu a bakin ciki, Fasto Suleiman

A wani labarin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce Fulani ba ‘yan ta’adda ba ne.

Ya fadi haka ne a Abuja jiya yayin ziyarar girmamawa ga ma'aikatan gudanarwa da sauran ma'aikatan Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Daily Trust ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.