Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka (Hotuna)

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa a kalla 'yan Najeriya 80,000 ke mutuwa daga cutar daji duk shekara. A ranar da ake tunawa da cutar daji duk shekara, wacce yau ne 4 ga watan Fabrairu, an tattara wasu sanannun 'yan Najeriya da suka rasu sakamakon cutar daji.

(1) President Umaru Yar’Adua

Tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua ya rasu ne sakamakon cutar daji a watan Mayu na 2010 bayan shekarun da ya dauka yana fama da ciwon bayan kasa sauke nauyin mulkin da yayi na dogon lokaci.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Marigayi Umaru Musa Yar'adua
Asali: UGC

(2) Dr. Olusola Saraki

Olusola Saraki ne shugaban majalisar dattijai karo na biyu. Ya rasu ne sakamakon ciwon dajin wanda dansa Olaolu ya tabbatar da hakan. Ya tabbatar da cewa babban dan siyasan jihar Kwara din ya rasu ne bayan shekaru biyar da yayi yana fama da cutar. Ya rasu ne ranar 14 ga watan Nuwamba 2012.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Marigayi Olusola Saraki
Asali: UGC

(3) Maryam Babangida

Maryam Babagida ita ce matar tsohon shugaban kasan mulkin soji, Ibrahim Babangida, Rayuwarta ta kare ne bayan da cutar daji ta kashe ta a ranar 27 ga watan 2009.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Maryam Babangida
Asali: Facebook

(4) Gani Fawehinmi

Babban mai rajin kare hakkin dan Adam din dan siyasa, Gani Fawehinmi ya yi gogayya da manyan soji wadanda ake jin tsoro a wancan lokaci. Amma kuma daga baya ya rasu ne sakamakon cutar daji. Ya rasu ne a rana 5 ga watan Satumba na 2009 bayan yayi fama da sankarar huhu.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Marigayi Gani Fawehinmi
Asali: Twitter

(5) Yinka Craig

Babban dan jarida ma'aikacin gidan talabijin na NTA ya yi gwagwarmaya da cutar daji amma sai ya rasu a ranar 23 ga watan Satumba na 2008. Ya rasu ne asibitin Mayo da ke Rochester a Minnesota da ke Amurka.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Yinka Craig
Asali: Twitter

(6) Yusuf Jibo

Yusuf Dabo tsohon daraktan yanki ne an gidan talabijin din Najeriya na NTA. Ya rasu ne sakamakon gwagwarmaya da yayi da cutar kansar hanji a watan Disamba na 2010.

(7) Sonny Okosun

Sonny Okosun babban mawaki ne kuma ya bara wanna sana'ar ne bayan rasuwarsa a ranar 24 ga watan mayu na 2008. A lokacin yana da shekaru 61 ne kuma ya sha jinya sakamakon cutar daji. Ya rasu ne a Amurka inda ya je neman shawara sakamakon rashin lafiyarsa da ke kara tsanani.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Sonny Okosun
Asali: Twitter

(8) Clara Oshiomhole

Clara ita ce marigayiyar matar shuagabn jam'iyyar APC, Adam Oshiomhole. Ta rasu ne a ranar 8 ga watan Disamba 2010 sakamakon fama da cutar kansa da tayi. Ta rasu ne ana saura kwanaki 11 bikin diyarta.

Fitattun 'yan Najeriya 8 da ciwon 'kansa' ya hallaka
Clara Oshiomhole
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: