Igbo Za Su Sokoto Neman Afuwa Kan Juyin Mulkin da Ya Yi Ajalin Sardauna? Gaskiya ta fito

Igbo Za Su Sokoto Neman Afuwa Kan Juyin Mulkin da Ya Yi Ajalin Sardauna? Gaskiya ta fito

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta musanta rade-radin cewa za ta nemi afuwar 'yan Arewa kan juyin mulkin 1966 da aka gudanar
  • Kungiyar ta ƙaryata labarin cewa ta na shirin zuwa har jihar Sokoto domin neman afuwa a juyin mulki daya ya ajalin manyan 'yan Arewa
  • Shugaban kungiyar, Cif Emmanuel Iwuanyanwu shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a birnin Owerri da ke jihar Imo a karshen mako

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi martani kan juyin mulki da ake zargin kabilar Igbo ta yi a shekarar 1966.

Kungiyar ta musanta cewa ta shirya zuwa jihar Sokoto domin ba da hakuri kan juyin mulkin da ya afku.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Kabilar Igbo ta yi martani kan zuwa Sokoto game da juyin mulki
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi fatali da rade-radin za ta je Sokoto ba da hakuri kan juyin mulkin 1966. Hoto: AYCOMEDIAN.
Asali: Getty Images

Martanin ƙabilar Igbo kan zuwa Sokoto

Shugaban kungiyar, Cif Emmanuel Iwuanyanwu shi ya bayyana haka a karshen mako a Owerri babban birnin jihar Imo, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iwuanyanwu ya ce babu kamshin gaskiya kan rade-radin cewa kungiyar za ta je Sokoto domin ba 'yan Arewa hakuri kan juyin mulkin.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar IPOB ta bayyana cewa Ohanaeze Ndigbo ta shirya zuwa Sokoto a kokarin ba 'yan Arewa hakuri kan abin da ya faru a 1966.

Juyin mulkin ya yi sanadin sojoji da dama da kuma manyan yankin Arewa ciki har da Sir Abubakar Tafawa Balewa da Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Sai dai shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya musanta rade-radin inda ya ce babu batun wanna labarin, cewar rahoton ThisDay.

Ndigbo ta ce babu neman afuwar Arewa

Kara karanta wannan

"Ya kware a cin amana": APC ta ja kunnen Tinubu kan sake jiki da gwamnan PDP

"Ba zamu taba zuwa rokon wani ba, an hallaka kabilar Igbo da dama a lokacin, ba mu da alaka da juyin mulkin 1966 saboda wannan sha'ani ne na sojoji."
"Wannan labari ba gaskiya ba ne, wanda ya yada rahoton ma ya ba da hakuri, abin da ya faru kawai mun yi ganawa a Enugu domin samar da zaman lafiya ga mutanenmu a Legas da sauran wurare."
"Igbo ba su kashe kowa ba, ba Igbo ba ne suka yi juyin mulki, duk wadanda aka kashe sojoji ne suka hallaka su ba Igbo ba, ba mu da alaka da hakan saboda sojoji ne suka yi juyin mulki ba Igbo ba."

- Emmanuel Iwuanyanwu

Iwuanyanwu ya kara da cewa babu wanda a cikin ƙabilar Igbo ya bukaci Nzeogu ya yi juyin mulki kamar yadda babu wanda ya fadawa sauran wadanda suka yi juyin mulki a Najeriya.

Kabilar Igbo ta bukaci afuwa daga Gowon

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta koka kan yadda Borno ke biyan 'yan fansho N4,000 a wata

Kun ji cewa kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bukaci tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya nemi afuwar kabilar Igbo.

Kungiyar ta bukaci hakan bayan zargin Gowon yana da hannu a kisan 'yan kabilar Igbo yayin yakin basasa da aka gudanar a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.