Zuri’ar Yar’adua: Gidan da Aka Samu Janar, Shugaban Kasa, Gwamna, Sanata da Minista
Abuja - Za a dade tarihi bai manta da labarin gidan Malam Musa Yar’adua ba, saboda rawar da suka taka a cikin gwamnatin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali Yar'adua unguwa ce a garin Katsina wanda yanzu tayi suna a duk duniya.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Wannan rahoto ya tattaro jerin gidan dangin Yar’adua da kuma mukaman da suka rike.
1. Musa Yar’adua
Marigayi Musa Yar’adua ya yi Ministan harkokin Legas da na fansho a zamanin gwamnatin Abubakar Tafawa Balewa, yana cikin kusoshin NPC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin yana raye, an nada shi sarautar Tafidan Katsina, daga baya ya zama Mutawalle. ‘Dan siyasar ya taba zama ‘dan majalisar tarayya,
2. Shehu Musa Yar’adua
Shehu Musa Yar’adua wanda yaron Musa Yar’adua ne ya zama shugaban hafsun sojoji a gwamnatin sojin Olusegun Obasanjo a 1976.
Bayan ya yi ritaya, Janar Shehu Musa Yar’adua ya shiga siyasa kuma har ya kusa kai ga samun takarar shugaban kasa a SDP a zaben 1993.
3. Ummaru Musa Yar’adua
Marigayi Ummaru Musa Yar’adua wanda kanin Shehu Yar’adua ne, ya yi nasarar zama gwamnan jihar Katsina a inuwar PDP a 1999.
Daga gidan gwamnatin Katsina sai ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2007. Tsohon shugaban Najeriyan ya rasu a kan mulki a 2010.
4. Murtala Shehu Yar’adua
Bayan rasuwar Ummaru Musa Yar’adua, sai shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada Murtala Shehu Yar’adua a matsayin Ministansa.
Murtala Yar’adua wanda shi ne babban ‘dan Shehu ya zama karamin ministan tsaro a 2010, ya hau wannan kujera bai cika shekara 40 ba.
5. Abdulaziz Musa Yar’adua
A dangin Yar’adua wanda yake cikin gwamnati a yau shi ne Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua wanda kanin tsohon shugaban kasa ne.
Sanatan na Katsina ta tsakiya ya yi aikin soja har ya kai matakin Kanal kafin shiga siyasa, yana cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulki.
Mulkin Jonathan bayan Yar'adua
Kwanan nan aka samu labari Ummaru Musa Yar'adua bai bar Najeriya ba sai da ya amince Goodluck Jonathan ya zama shugaban riko.
An yi ta yada cewa tsohon shugaban ya hana mataimakinsa rike madafan iko da yake ciwon ajali, Abdulaziz Yaradua ya karyata hakan.
Asali: Legit.ng