An Shiga Murna Yayin da Kayan Abinci Ya Sauko a Jihohin Arewa 3, an Bayyana Farashi

An Shiga Murna Yayin da Kayan Abinci Ya Sauko a Jihohin Arewa 3, an Bayyana Farashi

  • Yayin da ake fama da tsadar kayayyaki musamman bangaren abinci, an fara samun sauki a wasu jihohin Arewacin Najeriya
  • Jihohin da aka samu saukin idan aka kwatanta da kwanakin baya sun hada da Gombe da Jigawa da kuma jihar Bauchi
  • Legiti Hausa ta tattauna da wasu masu siyar da kayan abinci a Gombe kan farashin kayayyakin a bangarensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Da alamu an fara samun sauki a wasu jihohin Arewacin Najeriya musamman bangaren hatsi a kasuwanni.

Farashin kayan ya ɗan ragu da 10% a jihohin Gombe da Jigawa da Bauchi kamar yadda mazauna garuruwan suka tabbatar.

Farashin abinci ya fara sauƙa a wasu jihohin Arewacin Najeriya
An samu saukar farashin abinci a jihohin Gombe da Bauchi da Jigawa. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Nawa ne farashin kayan abinci a Gombe?

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Wannan na zuwa ne bayan tashin farashin kayan a kwanakin baya wanda ya rikita 'yan kasar, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Gombe, shinkafa mai nauyin kilo 50 ta sauko zuwa N66,000 daga N82,000 a kwanakin baya.

Haka nan buhun shinkafar gida wanda ake siyarwa kan kudi N130,000 ta sauko zuwa N120,000 a yanzu.

Har ila yau, kwanon wake da ake siyarwa kan kudi N1,600 yanzu ya saiko zuwa N1,400 wanda hakan ke nuna an samu sauki.

Yayin da a kasuwar Wunti da ke jihar Bauchi, ana siyar da buhun masara N58,0000 yayin da wake ja sauko zuwa N75,000 da kuma waken suya N32,000.

Yadda farashin abinci ya ke a Jigawa

Har ila yau, a kasuwar hatsi da ke Dutsen jihar Jigawa, ana siyar da shinkafar gida N140,000 idan aka kwatanta da N160,000 a baya.

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

Sai kuma buhun gero ana siyarwa da shi a kan kudi N68,000 a madadin N72,000 da ake siyarwa a baya, cewar Pulse.

Wani dan kasuwa a Bauchi, Danjuma Jahun ya ce hakan bai rasa nasaba da matakan da gwamnati ta ke ɗauka kan masu boye kayan abinci.

Munka'ila Isa da ke kasuwar hatsi shi ya ce bisa ga dukkan alamu kayan abinci za su ci gaba da sauka ganin yadda ake samun yawan kayan a kasuwa.

Tattaunawar wakilin Legit Hausa da masu abinci

Legiti Hausa ta tattauna da wasu masu siyar da kayan abinci a Gombe kan farashin kayayyakin a bangarensu.

Hajiya Altine ta tabbatar da cewa an samu faduwar farashin idan aka kwatanta da kwanakin baya.

"A da muna siyar da kwanon wake N1,500 amma yanzu ya sauko har N1,400 yayin da shinkafa da ake siyarwa N1,600 zuwa N1,700 a yanzu kuma N,1,400

- Hajiya Altine

Kara karanta wannan

CBN ya ba Gwamnati da 'yan majalisu na da laifi a hauhawar farashin kayan abinci

Yahaya Muhammad da ke siyar da kayan hatsi ya ce tabbas an samu raguwar farashin kuma ana sa ran zai yi kasa duk da dai ba a shiga damina sosai ba.

Tinubu ya magantu kan daukar matakai

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana himmatuwarsa wurin inganta Najeriya wurin ci gaba daukar muhimman matakai.

Tinubu ya ce zai ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri ko da kuwa za a shiga halin kunci na wani dan lokaci idan za a samu abin da ake nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel