An Taso Keyar 'Yan Najeriya 155 Zuwa Legas Bayan Sun Tafi Ci Rani a Kasar Waje
- Yan Najeriya kimanin 155 hukumar kula da hijira ta duniya (IOM) ta shige gaba aka dawo da su gida daga Libya inda su ke ci rani
- Cikin wadanda aka dawo da su mata sun fi yawa da yawansu ya kai 111 da maza 29, sai yara kanana guda 11 da kuma jarirai guda hudu
- Hukumar kula da hijira ta duniya (IOM) ce ta yi uwa da makarbiya wajen dawo da yan ci ranin gida wanda ta mika su hannun NEMA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ikeja, Lagos-Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa an dawo da yan ci rani 155 da su ka makale a Libya.
Hukumar NEMA ta ce an samu nasarar dawo da mutanen ne ta cikin shirin hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) a jiya Talata.
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na X a nemanigeria, hukumar ta ce jirgin Al Buraq ne ya dauko yan Najeriya, kuma ya sauke su a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Ikeja, babban birnin Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mata sun fi yawa a zuwa Libya
Daga mutanen da hukumomin NEMA da IOM su kayi nasarar dawo da su gida Najeriya akwai mata da maza da kananan yara.
A rahoton da Leadership News ta wallafa, yawan matan da aka dawo da su Najeriya ya kai 111, wanda ke nuna cewa mata da yawa na tafiya ci rani.
Sai kuma jarirai hudu, yara 11 da maza 29 da aka dauko daga sassa daban-daban na Libya.
A cewar hukumar NEMA, duk wadanda su ka samu biyo jirgin sun yi murna kwarai da ceto su daga mummunan yanayin da aka yi.
Mace ta zama shugabar NEMA
Mun kawo labari cewa a karon farko cikin shekaru 25 cewa mace ta zama shugabar NEMA mai bayar da agajin gaggawa, wanda hakan ya ja hankali sosai.
Nadin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Zubaida Umar ya ba ta damar zama mace ta farko da ta shugabanci hukumar tun shekarar 1999.
Asali: Legit.ng