Arewacin Najeriya Ya Fi Ko Ina Yawan Yara Marasa Zuwa Makaranta a Duniya, in Ji NGF
- Kungiyar gwamnonin Arewa (NGF) ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin
- NGF ta bayyana hakan a yayin taronta karo na biyu da ya gudana a jihar Kaduna, tana mai cewa hakan na kawo koma baya ga yankin
- A wannan taron, gwamnonin sun tattauna kan kalubalen da suke fuskanta a yaki da ‘yan fashin daji, garkuwa da mutane da dai sauran su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Kungiyar Gwamnonin Arewa, NGF, ta bayyana cewa Arewacin Najeriya ce ke kan gaba a yawan yara marasa zuwa makaranta a duniya.
Shugaban kungiyar NGF, Yahaya Inuwa ya nuna damuwa kan yadda yawan yara marasa zuwa makaranta ke zama barazana ga duk wani ci gaba a Arewacin kasar.
Gwamna Yahaya Inuwa, ya bayyana hakan a yayin taron kungiyar gwamnonin Arewa a jihar Kaduna, gidan talabijin na AIT ya ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da aka tattauna a taron NGF
A yayin taron kaddamar da kungiyar gwamnonin Arewa a ranar 15 ga watan Disamba, 2023, gwamnonin sun tattauna kan matsalolin da suka shafi yankin.
A lokacin, tattaunarsu ta fi karkata kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro, muhalli, ilimi da dai sauransu.
Amma a wannan taro na biyu, gwamnonin sun tattauna ne kan kalubalen da suke fuskanta a yaki da ‘yan fashin daji, garkuwa da mutane da dai sauran matsalolin tsaro.
Jihohin da matsalar tsaro ta fi kamari
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya jaddada kiransa ga gwamnonin Arewa da su samar da dabarun bai daya domin magance matsalar rashin tsaro a yankin, rahoton jaridar Vanguard.
Gwamna Yahaya Inuwa na jihar Gombe, ya nuna juyayi da goyon baya ga al’ummar jihohin Kaduna, Neja, Zamfara, Katsina da Filato, wadanda ke fuskantar matsalar tsaro.
Ya yi nuni da cewa, ci gaban tattalin arziki shine jigon magance matsalar rashin tsaro, yana mai cewa tilas ne yankin ya sanya hannun jari kan muhimman ababen more rayuwa.
Gwamnan Imo ya nada kansa kwamishina
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya nada kansa mukamin kwamishinan filaye na jihar.
A yayin rantsar da kwamishininonin a gidan gwamnatin jihar da ke Owerri, Uzodimma ya ce ya ba kansa mukamin ne saboda kare ma'aikatar daga badakalar da ta fada a baya.
Asali: Legit.ng