Yara fiye da Miliyan 13 ba su zuwa Makaranta a Najeriya – UNICEF

Yara fiye da Miliyan 13 ba su zuwa Makaranta a Najeriya – UNICEF

- Adadin marasa zuwa karatu a Duniya fiye da miliyan 20 a Duniya

- A ciki akwai yara miliyan 13 marasa zuwa makaranta a Najeriya

- Arewacin Najeriya na daga cikin inda ake fama da wannan matsala

Yara fiye da Miliyan 13 ba su zuwa Makaranta a Najeriya – UNICEF
UNICEF tace akwai miliyoyin yara da ba su zuwa karatu a Najeriya
Asali: UGC

Kungiyar Majalisar dinkin Duniya mai kula da sha’anin kananan yara watau UNICEF ta bayyana adadin wadanda ba su zuwa makarantar Boko a Najeriya. Jihohin Arewa sun na cikin wadanda su ka fi fama da wannan babbar matsala.

Binciken da Kungiyar UNICEF tayi kwanan nan ya nuna cewa an samu karuwar wadanda ba su karatun Boko a Najeriya daga yara miliyan 10.5. Yanzu akwai akalla kananan yara miliyan 13.2 da su ke yawo a kan titunan a Najeriya.

KU KARANTA: Kananun yara fiye da Miliyan 1.3 ba su zuwa Makaranta a Kano

Wannan adadi dai ya zarce na kowace kasa a fadin Duniya daga cikin yara miliyan 20 da ke fama da rashin karatun Boko. Rikicin Boko Haram yayi sanadiyyar fatattakar mutane fiye da 50, 000 daga gidajen su Arewacin Najeriya.

Kwanaki kun ji cewa Jihar Kano ce kan gaba wajen yawan yara marasa zuwa makaranta. Jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya na Borno, Yobe da kuma Jihar Adamawa su na cikin wadanda su ka karu da yawan marasa zuwa karatu.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu Gwamnatin Najeriya tana kashe abin da bai haura Dala Biliyan 24 bane a harkar ilmin Boko. Masana sun bayana cewa wannan matsala na daga cikin abin da ke kawo dakushewar tattalin arziki a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel