Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Hakika rawa wata abace da ke nuni da nishadi ko kuma jin dadi kuma akan yi ta ne idan wani abun jin dadi ya samu mutum ko kuma a lokuttan bukukuwa.

Ko shakka babu ita ma al'ummar Hausawa kamar yadda aka san su da dadadden tarihi musamman ma da fannin al'adu da kuma zamantake, ta na da na ta kalar rawa da ake yi idan har bukatar hakan ta taso.

Legit.ng ta tattaro maku wasu rabe-raben kalar rawar gargajiya a kasar Hausa:

1. Rawar Koroso

Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa
Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Wannan rawar tana da dadadden tarihi sosai don tana daga cikin ababen alfaharin bahaushe tun lokacin da ake kira kunne ya girmi kaka.

Rawar na da wani irin fasali ne wanda mutane da dama sanye da kayayyaki iri daya da kuma ababen kwalliya na karafa a jikin su ke yi kuma a lokaci guda domin ta kayatar.

Ba bu takamaiman lokacin da aka fara yin ta amma dai akan yi ta ne a lokacin bukukuwa don nishadin mahalarta.

Maza da mata duka na yi rawar.

2.Rawar Bankaura

Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa
Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Ita kuma wannan kamar yadda sunan na ta yake, rawa ce da ake yi ba tare da wani ainihin takamaiman tsari ba duk kuwa da cewa masu yin rawar sukan sanyan kaya iri daya ne wajen yin ta.

Ita ma wannan rawar akan yi ta ne a yayin bukukuwa da wajen durin aure kuma tana nishadantarwa musamman ma ganin yadda masu yin ta kan sanya tufafi irin na ban dariya.

Maza ne suka fi yin irin wannan rawar.

3. Rawar 'yan matan amarya

Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa
Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Ita kuma wannan kamar yadda sunan ta ya gwada ana yin ta ne a tsakanin 'yan matan amarya a yayin bukin aure.

Ita wannan rawar 'yan mata ne ke jera layi sanye da sabbin tufafi masu kayatarwa su rika tikar rawa lokacin muranar bukin aure tare kuma da saka amaryar a tsakiya.

A yayin rawar, 'yan matan kan yi da'ira su rika zagaya amaryar suna rera wakokin nishadi cikin murana da annashuwa.

4. Rawar Sangaya

Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa
Kayatattun kalar rawar gargajiya 4 a kasar Hausa

Ita kuma wannan rawar a iya kiranta ta zamani domin kuwa a kwanan nan ne aka fara yin ta.

Rawar ta samo asali ne daga wani wasan kwaikwayo na Hausa da aka yi shekarun baya cikin wani salo mai ban sha'awa.

Mata da maza duka suna yin rawar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng