'Yan Ta'adda Sun Baƙunci Lahira a Hanyar Zuwa Kai Hari Kan Mutane a Jihar Borno

'Yan Ta'adda Sun Baƙunci Lahira a Hanyar Zuwa Kai Hari Kan Mutane a Jihar Borno

  • Ƴan ta'adda sun baƙunci lahira yayin da suka yi yunƙurin kai hari a kauyen Mashurori da ke jihar Borno
  • Dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin guiwar jami'an rundunar JTF sun kashe ƴan ta'adda biyu tare da kwato miyagun makamai
  • Wannan nasara na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun kashe dakarun sojoji tare da sace kaftin a jihar Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe 'yan ta'adda biyu a jihar Borno.

Kamar yadda rahoton Channels tv ya kawo, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan ne yayin da suke kan hanyar zuwa kai farmaki a kauyen Mashurori.

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin addinin da 'yan bindiga suka sace ya shaki iskar 'yanci

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun halaka yan ta'adda, sun kwato muggan makamai a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sashin yaɗa labarai na rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ya fitar ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta bayyana cewa sojojin sun samu wannan nasara ne tare da haɗin guiwar rundunar ƴan sa'kai JTF yayin da suka fita sintirin tsaftace yankin.

A cewar rundunar sojin, bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri, dakarun sojoji suka ɗana tarkon kwantan ɓauna domin daƙile yunƙurin ƴan ta'addan.

Sojoji sun ƙwato makamai

Yayin musayar wuta da ƴan ta'addan, sojoji sun samu nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, Magazines biyu, harsashai na musamman, da kuma babur da ‘yan ta’addan ke amfani da shi.

Sojojin sun kuma kwato tikitin karbar haraji da tsabar kudi N60,000 da ake kyautata zaton suna da alaka da ayyukan karbar kudaden haram na ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Shugaban sojojin kasa ya aika da sabon gargadi ga 'yan ta'adda

An kashe sojoji a Neja

Wannan nasara na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ƴan bindiga sun halaka sojoji shida a jihar Neja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Legit Hausa ta rahoto cewa yayin harin da ya yi ajalin sojojin, maharan sun kuma yi garkuwa da wani Kyaftin din soja a kauyen Roro da ke jihar a ranar Juma'a.

Najeriya ta waiwayi ƴan Boko Haram

A wani rahoton kuma Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tuni ta ci gaba da gurfanar da ƴan Boko Haram da ta kama a gaban ƙuliya domin a hukunta su.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu ne ya tabbatar da haka a wurin taron yaƙi da ta'addanci a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel