"Shi Ke Haukata 'Yan Kasa", Malamin Addini a Kaduna Ya Ja Kunnen Tinubu Kan Halin Kunci
- Fasto Matthew Ndagoso da ke jihar Kaduna ya bayyana illar da tsadar rayuwa da rashin tsaro ya yi ga jama'ar Najeriya
- Faston ya ce yunwa da halin kunci da ake ciki shi ya sake jefa mutane cikin halin rashin lafiyar kwakwalwa a kasar
- Ya kuma koka kan yadda aka shafe fiye da shekaru 13 a kasar ana fama da matsalolin tsaro da rikicin addini da kabilanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Fitaccen Fasto a jihar Kaduna, Rabaran Matthew Ndagoso ya bayyana illar da rashin tsaro da wahala ke yi ga 'yan Najeriya.
Faston ya ce tsadar rayuwa da tashin tsaro shi ke kara tabawa 'yan kasar kwakwalwarsu.
Wasu matsaloli ke cutar da 'yan Najeriya?
Malamin ya bayyana haka ne a Kaduna a yau Juma'a 26 ga watan Afrilu yayin wani babban taro, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matthew ya ce cire tallafin mai da wasu tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu su suka kara jefa al'umma cikin wannan hali da suke ciki, cewar new Telegraph.
Ya ce kasar cikin shekaru 13 ta fuskanci matsalolin tsaro da hare-haren 'yan bindiga da rikicin kabilanci da na addini da kuma shaye-shaye.
"Mutane da dama sun rasa guraben ayyukansu da gidajensu da kuma kauyukansu."
"Yunwa da rashin abinci mai gina jiki ya yi ajalin mutane da dama a kasar, ya jawo mutane sun shiga ɗimuwa da bakin ciki da rashin sanin mene gobe za ta haifar."
- Mathew Ndagoso
Shawarar da ya bayar kan tabin kwakwalwa
Malamin addinin ya kuma zargi rashin tsaro da jefa mutane cikin halin rashin lafiyar kwakwalwa wanda ya hada da yunwa a kasar baki daya.
Ya bukaci gwamnati da ta samar da mafita kan yawan marasa lafiyar kwakwalwa a kasar wanda musabbabinsi shi ne rashin tsaro da tsadar rayuwa.
Fasto ya shawarci Tinubu kan Boko Haram
Kun ji cewa shugaban cocin Evangelical Spiritual, Elijah Ayodele ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta mayar da dazuzzukan 'yan Boko Haram su zama gonaki.
Fasto Ayodele ya bayar da shawarar ne a ranar 18 ga watan Fabrairu, yayin bikin cikar cocin shekaru 30 a jihar Legas.
Asali: Legit.ng