Shirin Ba Ɗalibai Rancen Kuɗi; Tinubu Ya Naɗa Jim Ovia a Matsayin Shugaban NELFund
- Shugaba Bola Tinubu ya nada wanda ya kafa bankin Zenith, Jim Ovia, a matsayin shugaban hukumar bayar da lamunin ilimi ta Najeriya
- Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar da sanarwar wannan nadin a ranar Juma'a, 26 ga watan Afilu
- Sanarwar ta ce Ovia zai yi aiki tukuru domin ganin cewa dalibai da matasan Najeriya sun sami ilimi mai zurfi da kwarewa a sana'a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada wanda ya kafa bankin Zenith, Jim Ovia, a matsayin shugaban hukumar bayar da lamunin ilimi ta Najeriya (NELFUND).
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Juma'a, wadda Dada Olusegun ya wallafa a X (Twitter), ta tabbatar da nadin Ovia.
Kadan daga tarihin rayuwar Jim Ovia
A cewar sanarwar:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ovia shi ne ya kafa daya daga cikin manyan bankunan Najeriya kuma abin koyi da 'yan kasuwa da ke girmamawa, yayin da ya himmatu wajen ƙarfafa guiwar matasan kasar.
"Shi tsohon dalibi ne na makarantar kasuwanci ta Harvard kuma yana da digiri na biyu a fannin kasuwancin daga jami'ar Louisiana."
Manufar hukumar NELFund
Shirin ba ɗalibai rancen kuɗin karatu an kaddamar da shi domin tabbatar da dorewar ilimi mai zurfi da bunkasa fasahar sana'o'i ga dukkan ɗalibai da matasa na Najeriya.
Hukumar ba da lamunin ilimi ta Najeriya, wacce za ta tabbatar da cimma muradin gwamnati na dorewar ilimi na buƙatar ƙwararrun 'yan Najeriya da za su jagorance ta.
Tinubu ya dora yakini a kan Ovia
Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Tinubu na da yakinin cewa:
"Mr. Ovia zai yi amfani da ilimi gami da ƙwarewarsa wajen ganin cewa daliban Najeriya sun sami gudunmawa da suke bukata wajen neman ilimi mai zurfi.
"Sabon shugaban hukumar zai taka rawa wajen ganin dalibai daga ko ina a Najeriya ba tare da la'akari da inda suke fito ba sun sami ilmi da kwarewar sana'a domin zama jakadu na-gari."
Karanta sanarwar a kasa:
Sharrin dandalin sada zumunta
Rahoto ya zo cewa dandali da shafukan sada zumunta sun kusa raba Ministan Muhammadu Buhari da matarsa a shekarar 2018.
Wani lokaci ne a 2018, Lai Mohammad ya zo Legas aiki daga Abuja, sai matarsa ta bijiro masa da zancen satar kudi daga asusun kasa.
Asali: Legit.ng