Gwamnatin Tarayya ta Fara Tunanin Hana Fursunoni Tserewa daga Kurkuru
- Gwamnatin tarayya ta ce yanzu ta na tunanin yadda za a dakile tserewa da fursunoni su ke yi daga gidajen yarin da ke kasar
- Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce akwai bukatar sauyawa daurarrun matsuguni
- Ya bayyana cunkoso da ya ce akwai a gidajen yarin na daya daga matsalolin da su ke fuskanta, kuma za a magance a nan gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru shida. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Neja-Gwamnatin tarayya ta ce ta na tunanin sauyawa daurarrun da ke fursun din Suleja matsuguni bayan wasu daga cikinsu sun tsere.
A kwaf daya, daurarru kimanin 119 ne su ka tsere bayan ruwa da iska sun lalata wani bangare na fursun din.
A ziyarar da Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya kai fursun din a Alhamis din nan, ya ce akwai bukatar a sauya musu matsuguni zuwa wuri mai kyau, kamar yadda Channels Television ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai cunkoso a fursunoni inji Minista
Minista Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa kafin mamakon ruwan saman, akwai fursunoni 499 a gidan yarin da aka gina tun shekarar 1914.
Ya ce an gina fursun din ne saboda masu laifi 250 kadai, amma an zuba fursunonin da su ka ninka wannan adadi.
Olubunmi Tunji-Ojo ya kara da cewa wannan na nuna yadda ake samun cunkoso a gidajen yarin Najeriya.
Ya ce cikin daurarru 119 da su ka tsere, an samu nasarar damke goma, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kuma ana ci gaba da farautar sauran mutane 109 da yanzu haka ke a mala.
Ministan ya kuma bayyana shirin da gwamnati ke yi na samar da gidajen yari masu inganci da yalwa.
Fursunoni sun tsere a Neja
Mun kawo mu ku yadda wasu fursunoni su ka tsere daga gidan ajiya da gyaran hali da ke karamar hukumar Suleja a jihar Neja.
Lamarin ya afku ne biyo bayan mamakon ruwan sama da ya zaftare wani bangare na katangar gidan, wanda wasu daga daurarrun su ka yi amfani da damar wajen guduwa.
Asali: Legit.ng