Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Ramadaniyyat 1443: Azumi Cikin Tsananin Zafi, Tare da Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo malami ne a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Bayero da Kano kuma shugaban cibiyar nazarin addinai a jami'ar.

Azumi Cikin Tsananin Zafi

1. Azumin watan Ramadan na wannan shekara ta 1443\2022 ya zo a cikin yanayin tsananin zafi. Sau tari zafin rana yakan wuce daraja 40 a ma'aunin selshiyos (Celsius).

2. Babu shakka yin azumi a irin wannan yanayi mai zafi, yana xauke da dumbin lada ga duk wanda ya tsarkake niyyarsa. Allah (SAW) ya yi wa sahabbai da suka fita yakin Tabuka a cikin tsananin zafi albishir da cewa:

(…Wannan kuwa saboda ba wata kishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su a kan hanyar Allah, kuma ba za su taka wani wuri ba da zai bata wa kafirai rai, kuma ba za su tafka wa abokan gaba wata hasara ba sai an rubuta musu lada saboda shi (wato kowane daya daga abubuwan da aka zana). Lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa). [Tauba, aya ta 120].

Kara karanta wannan

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

3. Don haka duk wata wahala da za ta samu mutum a dalilin biyayya ga Allah, to za a rubuta masa lada a kai, a kuma daga darajarsa.

An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Yanzu ba na nuna muku abin da Allah yake goge muku kurakurai da shi ba, yake kuma daga daraja da shi?" Sai suka ce: "E, muna so ya Manzon Allah. Sai ya ce: "Cika alwala a lokacin da rai ba ya so (wato lokacin sanyi), da yawan tattaki zuwa masallaci; da jiran salla bayan salla. Wannan shi ne ribadi, wannan shi ne ribadi. [Muslim#252].

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakanan Annabi (SAW) ya fada wa matarsa A'isha, Allah ya yarda da ita, cewa: "Gwargwadon wahalarki gwargwardon ladanki". [Muslim#1211].

4. Daga cikin abubuwan da za su ɗauke wa mumini jin wahalar azumi a cikin wannan yanayi na zafi, abubuwa ne guda biyar:

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

Na ɗaya, Tunawa da yawan ladan da mutum zai samu idan ya tsarkake niyyarsa.

Wata baiwar Allah daga cikin magabata na kwarai ta yi tuntube sai farcenta ya fita, sai aka ga ta yi dariya, tana cewa: "Dadin ladansa ne ya mantar da ni zafin ciwonsa".

Na biyu, Tuna azabar wutar jahannama da Allah ya yi wa masu laifi alkwarin shigar ta, domin tsananin zafi yana daga cikin hucin wutar jahannama, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira (RA). [Duba, Bukhari#3260 da Muslim#617].

Na uku, tuna girman wanda ya yi umarni da yin azumi, da tuna ranar tsayuwa a gabansa. Wannan zai rage wa bawa jin duk wata wahala ta yanayin zafin rana.

Na huɗu, halarto da cewa, Allah (SAW) yana ganin bawansa lokacin da yake tsaka da wannan bautar ta azumi, yana sane da duk irin wahalhalun da yake sha. Duk wanda ya sakankance da cewa, masoyinsa yana ganin irin wahalar da yake ciki saboda soyayyarsa, to wahalar takan zo masa da sauki, kamar yadda Allah (SAW) ya yi wa Manzonsa nuni da haka inda yake ce masa: (Ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka don ko lalle kana karkashin lurarmu) [Suratut Dur, aya ta 48].

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Na biyar, Nutse wa cikin soyayyar wanda ya yi umarni da yin wannan ibada ta azumi. Duk wanda zuciyarsa ta cika da son Allah (SAW), to zai so abin da yake so komai wahalarsa kuwa.

Allah (SAW) muke roka da ya karbi ayyukanmu ya ba mu cikakken lada a kai. Amin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel