Kaduna: Farashin Litar Fetur Ya Haura N1,000 Yayin da Aka Fara Dogon Layi a Gidajen Mai
- Ƙarancin man fetur ya ƙara jefa mutane cikin ƙaƙanikayi a jihar Kaduna yayin da ƴan bunburutu suka fara cin kasuwa
- Rahoto ya nuna cewa litar fetur ta kai N1,000 a hannun ƴan bunburutu kuma masu Napep da sauran ababen sufuri sun kara tsada
- Galibin ma'aikata da suka fito domin zuwa wurin aiki da ƴan kasuwa sun gamu da cikas saboda ƙarancin ababen hawa yau Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Wahalhalu sun kara tsananta ga mazauna jihar Kaduna musamman masu ababen hawa yayin da aka wayi gari da dogayen layuka a gidajen mai.
Ga dukkan alamu man fetur ya yi ƙaranci a jihar wanda ya tilastawa direbobi da masu ababen hawa sayen litar mai kan N1000 a hannun ƴan bunburutu.
Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa mafi akasarin ma'aikata da sauran mutane da suka fito da zummar tafiya wurin aiki ko sana'a sun shiga wahala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya faru ne sakamakon ƙarancin man fetur wanda ya sa da yawan ƴan haya kama daga ƴan Taxi da masu adaidaita sahu sun noƙe ba su fito aiki ba.
Galibin gidajen mai ba sa ba da man fetur ba, kuma ’yan kalilan da suka fito suna sayarwa sun ƙara tsada a farashin zuwa tsakanin N750 - N810 kowace lita.
Mutane sun koka da wahalar fetur
Wani mai abun hawa a Kaduna, Mohammed Amin, ya ce ya sayi rabin galan watau kimanin lita biyu kenan a kan N2,200.
A cewarsa ya fara tunanin ajiye motarsa ya koma amfani da na haya idan wannan matsalar ta ci gaba da tsananta.
Haka nan kuma an tattaro cewa su kansu masu ababen hawa na haya sun fara amfani da ƙarancin mai wajen ƙara kudin sufuri.
Sufuri ya ƙara tsada saboda tsadar fetur
Amina Isa, wata da ta saba hawa mota ta biya N100 daga gidan man NNPC zuwa roundabout, sannan ta ƙarisa wurin aikinta, ta bayyana cewa:
"Bayan tsayuwar sa'o'i uku babu abin hawa, ba ni da wani zaɓi face na hau wata Napep da direban ya nemi na biya N300 zuwa wurin da na saba zuwa."
Wani fasinja mai suna Moses Joseph ya ce ya biya N400 maimakon N200 daga Kakuri zuwa Ahmadu Bello Way.
Haka kuma, Misis Anna Yohanna da ta hau motar bas daga Goni Gora zuwa babbar kasuwar Kaduna, ta ce ta biya Naira 500 maimakon N250, Punch ta rahoto.
Ƙarancin fetur ya taɓa jihohi
A wani rahoton kuma, an ji n wayi garin Alhamis da ganin dogayen layin mai a wasu jihohin kasar nan ciki har da Kano, Gombe, Anambra da babban birnin tarayya Abuja.
Rashin samun man ya kara ta'azzara farashin ababen hawa yayin da wasu gidajen man su ka ku budewa ballantana su sayarwa masu bukata man fetur.
Asali: Legit.ng