Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC

Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC

  • Abdulwahab Eyitayo, babban kwamandan Div 7, ya ce a kalla 'yan ta'addan Boko Haram 8,000 ne suka tuba
  • Eyitayo ya ce hakan ta biyo bayan lugude da ragargazar da dakarun sojin Najeriya ke yi wa miyagun ne
  • Ya bukaci masu tausaya wa 'yan ta'addan da su shawarce su kan su mika wuya tun kafin lokaci ya kure musu

Borno - Mukaddashin babban kwamandan Div 7, Abdulwahab Eyitayo, ya ce sama da 'yan ta'addan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Borno.

Ya ce 'yan ta'addan sun mika wuya bayan fitowarsu daga maboyarsu a dajin Sambisa da sauran inda suke boye wa, Premium Times ta ruwaito hakan.

Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC
Fiye da 'yan Boko Haram 8,000 ne suka mika wuya tare da tuba, GOC. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Eyitayo, wanda shi ne kwamandan sashi na 1 na Operation Hadin Kai, ya bayyana hakan yayin ziyarar da daraktan yada labari, Onyema Nwachukwu da wata tawagar tsaro daga Abuja a ranar Talata a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Ina tabbatar muku za'a hukunta tubabbun yan Boko Haram: Kwamandan Operation Hadin kai

Ya ce tuban da tubabbun 'yan ta'addan suka yi babban cigaba ne kuma ya kara da cewa abun farin ciki ne da kuma jinjina da yadda sojin suka yi kokari, Premium Times ta ruwaito.

Kamar yadda yace, "Daya daga cikin dalilan da yasa miyagun ke tuba shi ya tsananta ruwan wuta da dakarun soji suka yi musu."
"Suna tuba ne saboda duk magidanci na son jin dadin iyalinsa, hakan yasa suke fitowa daga maboyarsu da iyalansa. Mun fara ganin alamu tun daga watan Yuni.
"Tsananta ragargazarsu ya toshe hanyoyinsu na samun kayayyakin bukata. Muna musu ruwan bama-bamai ta ko ina, hakan yasa suka fara mika wuya da kuma cutuka da suka addabi da yawa daga cikinsu.
"Hakan ya fi saboda daga karshe, dakarun za su kawar da dukkansu da masu tausaya musu," yace.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

GOC ya ja kunnen cewa, lokaci zai zo da babu damar da 'yan ta'addan za su iya tuba, ya yi kira ga masu tausaya wa 'yan ta'addan da su basu kwarin guiwar fitowa daga maboyarsu.

Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas

A wani labari na daban, sama da yara 300,000 ne suka rasa rayukansu a shekaru 12 da suka gabata sakamakon ta'addancin da ya addabi yankin arewa maso gabas, kiyasin kwanakin nan da UNICEF ta saki ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin Najeriya sun bayyana cewa ISWAP ta fara gangamin daukan matasa marasa aikin yi aiki domin tada zaune tsaye, Daily Trust ta ruwaito.

Kiyasin kwanan nan da UNICEF ta saki ya kara da bayyana cewa sama da mutum miliyan daya sun rasa gidajensu a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel