Gwamna Zulum Zai Rika Biyan Kowane Dalibin Jinya N30,000 Duk Wata a Jihar Borno

Gwamna Zulum Zai Rika Biyan Kowane Dalibin Jinya N30,000 Duk Wata a Jihar Borno

  • Gwamnatin jihar Borno ta sanar da fara biyan daliban jinya da ungozoma tallafin karatu na Naira dubu 30 duk wata a fadin jihar
  • Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ne ba bada sanarwar a jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin bikin kaddamar da tallafin karatu a Maiduguri
  • Ya kuma tabbatar da cewa bayan kudin alawus din wata-watan, za a kara wani kudin tallafi a cikin kudin makarantar da daliban za su rinka biya duk shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Gwanatin jihar Borno ta sanar da fara biyan daliban jinya da ungozoma tallafin karatu ga kowanne dalibi har N30,000 duk wata a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kwace lasisin rijiyoyin mai kan rashin biyan haraji

Governor Zulum
Gwamna Zulum ya ce dalibai 'yan asalin jihar Borno ne kawai za suci moriyar tallafin. Hoto: Professor Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Gwamnan jihar ne, Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da lamarin jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin bikin kaddamar da tallafin karatu wa dalibai 'yan asalin jihar Borno a Maiduguri, babban birnin jihar.

Adadin daliban da za su samu tallafin

A cewar jaridar Daily Trust, gwamnan ya tabbatar da cewa dalibai 997 da suka fito daga jihar ne zasu mori tallafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa tallafin anyi shine wa daliban lafiya domin karfafa musu gwuiwa da samar da wadatattun ma'aikatan lafiya a jihar.

Adadin kudin da gwamnati za ta kashe

Jawabin nasa ya nuna gwamantin za ta kashe jimillar N1.3b wa daliban domin tallafi.

Ya kuma bayyana cewa tallafin ya shafi kudin makaranta da alawus da za a rinka basu duk wata.

A cewar gwamnatin, daliban zasu rinka karban alawus din ne daga shekarar da suka fara karatu har su kammala.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya shiga sabuwar matsala yayin da majalisar Kaduna ta kafa kwamitin bincike

Gwamnan kuma ya yi alkawarin bada aiki nan take ga dukkan daliban da suka nuna bajinta a lokacin karatun nasu, cewar jaridar the Gurdian Nigeria

Gwman Zulum ya bawa manoma tallafi

A wani rahoton kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kirkiro shirin bada tallafi wa manoma a jihar ta hanyar samar da motoci da za su rinka kaisu gonaki.

Gwamnan ya samar da motoci guda 300 da za su rinka kai manoma zuwa gonaki domin saukaka musu da samar da wadataccen abinci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel